31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Bidiyon yaro tsaye cak kan mazaunan mahaifiyarsa yayin da take tafiya ya dauki hankula

LabaraiBidiyon yaro tsaye cak kan mazaunan mahaifiyarsa yayin da take tafiya ya dauki hankula
  • Wani bidiyo mai ban mamaki wanda mutane da dama su ka dinga wallafawa ya dauki hankalin jama’a da dama
  • A bidiyon, anga inda wani yaro ya ke tsaye cak akan mazaunan mahaifiyarsa yayin da ta ke ci gaba da tafiya a titi
  • Mutane sun yi ta cewa yaron yana da sa’a kwarai kasancewar da alamu yana kwasar nishadi yayin tsayuwar

An ga bidiyon wani yaro tsaye cak a mazaunan mahaifiyatsa yayin da take tafe shi kuma yana kwasar nishadi da yin hakan, Yen.com.gh ta ruwaito.

A bidiyon wanda hankulan jama’a da dama ya karkata akai, an ka matar tana tafea titi ba tare da dagewa ko kuma daure yaron da zani a bayanta.

Matar ta ci gaba da tafiyarta ba tare da damuwa ba kasancewar ta san babu matsala kuma ba zai fado daga wurin ba.

Bidiyon wanda wanda ya ga matar da dan ta ya dauka ya janyo mutane da dama su na yabon surar matar inda su ke cewa Ubangiji ya yi mata baiwa.

Wannan dalilin ne ya sanya su ka dauki bidiyon don su nuna wa ma’abota amfani da kafafen sada zumunta.

Sai dai abinda zai ba mai karatu mamaki shi ne yadda kowa yake tafe ba tare da mayar da hankalinsa kan ta ba, kamar abinda aka saba gani.

Yadda mazaunan roban da wata budurwa tayi ciko dasu su ka zame tana tsaka da rawa

Wata budurwa ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani bayan ta sanya mazaunan roba amma kuma su ka zame tana tsaka da rawa a wani fati, Adomo online ta ruwaito.

Budurwar ta je wata liyafa ne kuma ta sanya wata riga gajera mai kalar koriya da kuma farin takalmi rufaffe.

Tana tsaka da kwasar rawa tare da wani mutum kamar yadda sauran ‘yan matan da su ka je su ke kwasar rawa yayin da wasu kuma su ka tsaya a gefe su na ba idanunsu abinci.

Duk da yadda ta dauki wankan amma kuma abu guda ne ya gama kwafsata.

Yanayin yadda mazaunanta su ka zauna sun bai wa kowa mamaki don daga gani na roba ta sanya su ka zamiye saboda tsabar rawan da ta sha.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe