27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Talauci ko ƙeta: Yadda aka cafke wata mata na ƙoƙarin siyar da ɗan cikinta kan kuɗi N243k

LabaraiTalauci ko ƙeta: Yadda aka cafke wata mata na ƙoƙarin siyar da ɗan cikinta kan kuɗi N243k

An cafke wata mata bisa ƙoƙarin sayar da yaron ta mai shekara bakwai a duniya ga mutanen da bata san su ba kan kuɗi £4,000, (N243k)

Matar wacce ta haifi yara uku anyi zargin ta tallata ɗan na ta a matsayin na sayarwa a ƙoƙarin ta na biyan basussukan da ta ci. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Yadda aka cafke ta

Matar mai shekara 36 a duniya wacce aka kira kawai da Nargiza, ta haɗu da masu siya a wani shago domin sayar da ɗan ta amma masu siyan ƴan sakai ne na wata ƙungiyar hana bauta waɗanda suka zo mata a matsayin masu siyan yaron.

An kulle ta a ƙarƙashin dokokin ƙasar Rasha na hana safarar yara.

Nargiza tace ɗan na ta bai damu ba don a miƙa shi ga wasu iyalan akan kuɗi.

Kakakin ƙungiyar da ta ceto yaron ta hanyar zuwa a matsayin masu siya yace:

Har zuwa ƙarshe mun yi fatan cewa labarin ƙanzon kurege ne, cewa wannan wani sakaran wasa wani ne kawai ko damfarar samun kuɗi.

Sai dai lokacin da tawagar mu, tare da jami’an bincike muka tafi wurin cinikin, mun ga shaidar ana siyar da yaron

Nargiza ta karɓi kuɗin sannan ta bayar da yaron ga mutumin da bata sani ba.

Mijin matar na yanzu baya son yaron

An dai tafi da ita zuwa magarƙama yayin da ɗan na ta wanda ta samu a wurin tsohon mijinta sannan mijinta na yanzu baya son shi an tafi da shi asibiti.

Kakakin ya kuma ƙara da cewa:

Nargiza tayi bayanin cewa mijinta baya son babban ɗan ta, sai suka yanke shawarar siyar da yaron domin su biya basussukan su.

Wata mata ta sayawa mijin ta ‘yar bebin roba domin ta dinga maye gubinta idan bata nan

A wani labarin kuma wata mata ta siyawa mijinta ƴar bebin roba wacce zata dinga maye gurbin ta.

Wata mata da take matukar son mijin ta ,mai suna Char Gray ‘yar kasar Burtaniya ta sayawa mijin ta wata ‘yar bebin roba, wacce aka sa mata suna Dee, domin ta gamsar da mijin ta mai yawan sha’awa idan bata nan.

A fadar Coventry Telegraph, Grey din , ta yanke shawarar sayan ‘yar bebin ne bayan mijin nata mai matukar sha’awa, wanda aka bayyana sunan sa da Callum, ya shawararceta akan zai karo wadansu mata guda uku, waɗanda ita kuma sam ba ta gamsu da su shigo rayuwar su ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe