31.5 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Cima Zaune:Yadda ‘Yan Damfara Suka kirkiri majinyaciyar cutar kansa ta karya

IlimiCima Zaune:Yadda 'Yan Damfara Suka kirkiri majinyaciyar cutar kansa ta karya
b3d24e000d2ffb9c

Alexandria, wata yarinya mai shekaru 9 tana fama da ciwon daji in da aka ganta a bidiyo a shafukan sada zumunta tana neman taimako. “Don Allah, ku taimake ni, ba na son in mutu,” ana iya jin yadda Alexanderia ke roƙo a cikin bidiyon da aka wallafa a Facebook, YouTube har ma a wasu shafin tallace-tallace na google.
Bidiyon mai cike da ban tausayi inda aka ga Alexandria ‘yar kimanin shekara 9 wacce iyayenta suka kasance marasa karfi wadanda ke fafutukar biyan kuɗin magani.
Hawaye cike da fuskarta take bayyana cewa likitoci sun sanar da iyayenta cewa ciwon daji ya yadu a duk sassan jikinta.

Har a kafafen sada zumunta

Har a kafafen Facebook, YouTube da Google Ads duk an yada tallanta. Bidiyon ya kuma janyo cece-kuce a tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta, kamar yadda binciken gaskiya na gidan jaridar Premium Times webiste,inda aka gano cewar taimakon da kungiyar da aka fi sani da Netiv Halev ta ke nema game da yarinya mai dauke da cutar daji karyane.

Me yasa za ai Amfani da cutar kansa a matsayin hanyar samun kudi

Rahotanni sun bayyana cewa ciwon daji na daya daga cikin cututtukan da har yanzu likitoci ke fafutukar neman maganinsa.Rahotanni sun nuna cewa tana kashe mutane kusan 21,000 duk shekara a duk duniya.
Don haka, yin amfani da ciwon daji da kuma yarinya mai shekaru 9 wata hanya ce ta damfara kuma an shirya hakan ne yadda zai ja hankalin mutane sosai.
Shafin ya tattara fiye da martanin mutane kimanin 14,000, sharhi 6500 da kuma kimanin mutum 1,900 da suka yada a shafin Facebook har zuwa watan yuli 2022, a cewar Dubawa.Har ila yau, ta sami sharhin mutane akan YouTube sosai, wanda yana samu ra’ayoyi sama da miliyan 2.9 da 2,200 akan YouTube tare da masu biyan kuɗi sama da 3,410 a tashar da ta watsa bidiyon Jama’a da dama sun bayyana cewa sun bayar da gudunmawar da ta kai dala 10 kuma wata mata tace ta bayar kyautan dala daya inda nan take aka yashe mata ma’ajiyar ta.

Bayan shafe shekaru 67 a gidan yari an sallami wani tsoho da aka tsare tun yana dan shekara 15 amma yace ba inda zashi

Wani tsoho da ya shafe shekara 67 a gidan yarin Philadelphia, bayan an yanke masa hukuncin daurin rai da rai, ya nuna turjiya ta kin fita daga gidan yarin, bayan an sallame shi an yi masa afuwa.

Dalilin zuwan tsohon gidan yari
Tsohon mai suna Joseph Ligon, an daure shi ne tun yana ɗan shekara goma sha biyar, a sakamakon zargin kisan wadansu mutane biyu. Tun daga wancan lokaci Ligon ya rasa yancin sa na walwala.
A ranar 20 ga Fabarairun shekara ta 1953, a wajen wata liyafa, Ligon din da abokansa hudu suka yi wa mutane takwas fashi, inda suka kashe biyu daga cikin su har lahira.

Duk tsawon wannan lokaci , Ligon bai tura takaddar neman afuwa ba, wacce ita zata sa a sake shi daga gidan yarin, tare da sanya ido akan sa domin tabbatarda ganin bai sake shiga cikin wata matsala ba.

Baiyi tsammanin za’a iya yi masa afuwa ba
A cewar lauyansa, bai mika takardar neman afuwan ba ne saboda bai yi tunanin ya cancanci a sake shi ba, inda ya shafe shekaru 67 a gidan yari.

gidan yari
Bayan shafe shekaru 67 a gidan yari an sallami wani tsoho da aka tsare tun yana dan shekara 15 amma yace ba inda zashi
Har’ila yau, ya sake samun wata dama a shekarar 2016, amma sai ya gaza yin amfani da ita, saboda tunanin da yake dashi a baya na cewa bazai iya samun sassauci ba.

Idan aka sallami Joseph Ligon, zai tafi ya gudanar da rayuwar sa ba tare da sanya idon hukuma akan sa ba. Amma ya ki karbar afuwar da aka yi masa, bayan abokan zaman sa fursunoni sun amshi tasu afuwar da hannu biyu.

yana jin kurkuku tamkar gida a gareshi
Kasantuwar ya dade a gidan yarin, wadansu ma na ganin cewa bazai iya rayuwa a wani wuri ba kurkuku ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe