Ana zargin wasu ‘Ɓarayi’ sun kutsa gidan gwamnatin jihar Katsina sun sace kudi har naira miliyan N31m.
Wannan shi ne karo na biyu da aka yi irin wannan ta’asar ta sata a gidan gwamnati, wanda shine yakamata ya kasance ginin da yafi kowanne tsaro a faɗin jihar.
An taɓa tafka sata a ofishin sakataren jihar Katsina
A shekarar 2020, an sace maƙudan kuɗaɗe da suka kai miliyan N16m a ofishin Sakataren gwamnatin Katsina (SSG).
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa wata majiya daga gidan gwamnatin ta shaida cewa lamarin satar kuɗin ya faru ne tun a ranar 31 ga watan Yuli, 2022.
Majiyar wacce ta nemi a sakaya sunan ta tace wasu mutane da ba’a san ko suwaye ba sun kutsa ofishin mai kula da kuɗi na gidan gwamnatin, suka yi awon gaba da wasu kuɗi a cikin buhu.
A cewarsa, satar ta auku ne da daddare lokacin mai kula da kuɗin, Salisu Batsari, yana cikin ofishin.
Banga kyamarar CCTV ba amma kunsan tana daya daga cikin abubuwan da yan sanda zasu buƙata. Naji ance kyamarar ta ɗauki wani mutum ya rufe fuskarsa lokacin da ya kutsa Ofis ɗin ta cikin taga.” A cewar sa
An tabbatar da aukuwar lamarin
Wani hadimin gwamnan jihar Katsina, Al’Amin Isa, ya tabbatar da sace kudin ga manema labarai amma bai ce komai ba game da adadin kuɗin da aka rasa ba.
An miƙa rahoton lamarin ga ƴan sanda sannan ana cigaba da gudanar da bincike
Isa ya ƙara da cewa gwamnatin da hukumar ƴan sanda na kan bincike game da satar kuma babu tantama duk wanda ya aikata zai fuskanci fushin hukuma.
Yace a lokacin da lamarin ya auku da farko, gwamnati ta ɗauki matakai domin daƙile sake aukuwar hakan amma mutanen na da shegen wayau.
Ƴan sanda ba su ce komai ba kan lamarin
Duk da kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Gambo Isa, bai dawo da saƙon da aka tura a wayar sa domin jin ƙarin bayani dangane da lamarin, majiyar gidan gwamnatin ya ce an kama wasu jami’ai amma an sake su.
A ranar Litinin da gwamnati ta fahimci an sace kuɗin, cikin gaggawa ta shigo da ƴan sanda suka fara bincike. Mai kula da kuɗin da wasu ma’aikata da masu gadi dake aiki a ranar ƴan sanda sun gayyace su domin amsa tambayoyi.”
Da aka tambaye shi ko da gaske ƴan sanda sun saki waɗanda ake zargin, sai ya kada baki yace ba shi da masaniya kasancewar ba ya daga cikin masu yin binciken.
An kashe shugaban ‘yan ta’adda da matansa a harin da jirgin sama ya kai jihar Katsina
A wani labarin kuma an kashe shugaban ƴan ta’adda da matan sa a wani hari da jirgin yaƙi ya kai a jihar Katsina.
Rundunar sojin saman Najeriya, ta kai wani samame da safiyar Lahadi, inda ta yi nasarar kashe shugaban kungiyar ‘yan ta’adda da ke aiki a Zamfara, Abdulkarimu Faca-Faca tare da matansa biyu da manyan kwamandojin sa takwas.
An kai farmakin ta sama ne da misalin karfe 3 na safiyar Lahadi a kauyen su mai suna Marina, a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com