34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Babu abinda ku ka iya sai ‘gina tumbinku’, Peter Obi ga PDP da APC

LabaraiBabu abinda ku ka iya sai 'gina tumbinku', Peter Obi ga PDP da APC
  • Rikici na ci gaba da hautsinewa tsakanin manyan jam’iyyun Najeriya yayin da su ke kokarin yin kamfen don ganin jama’a sun zabe su a 2023
  • A ranar Alhamis, Peter Obi ya daura laifin lalacewar kasar nan akan jam’iyyar APC da PDP inda yace su ne sanadin wahalar da jama’a ke ciki
  • Tsohon gwamnan Jihar Anambra din ya shawarci jama’a akan dagewa wurin ganin sun ceto Najeriya ta hanyar zabar wadanda su ka dace.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Labour Party (LP) Peter Obi ya kwatanta tsarin gina kasar nan da APC da PDP su ke yi a matsayin ‘gina tumbi’, Legit.ng ta ruwaito.

A cewar tsohon gwamnan Anamb din ya bayyana cewa APC da PDP ne sanadin duk wata wahala da ‘yan Najeriya su ke ci a cikin shekaru 20 da su ka gabata, The Guardian ta ruwaito.

Obi ya bayyana hakan ne a taron jam’iyyar LP da aka yi a dakin taron kasa da kasa (ICC) da ke Abuja, ranar Alhamis, 11 ga watan Augusta.

“Tsarin kasar nan da PDP da APC su ka yi, tsari ne na gina tumbi kawai kuma bai kari kowa da komai ba sai wahala.

“A fahimtarsu dangane da gina kasa, kawai kalmashe dukiyoyin jama’a ne. Wannan kuma ba tsarin Peter Obi bane, ba kuma tsarin Yusuf Datti Baba-Ahmed bane. Kuma hakan ya yi cikas daga manufar LP,” a cewar Peter Obi.

Ya bukaci magoya bayansa da su tunatar da jam’iyyun adawar da cewa tabbas sai an bubbugo da tattalin arzikin kasar nan.

A cewar Obi, tsarinsa zai tallafawa talakawan Najeriya miliyan 100 wadanda za su fito don zabensa da kuma yaki don ganin kasar nan ta ci gaba.

Dalilan da yasa ba zan binciki gwamnatin Buhari da sauran gwamnatoci ba -Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarkashin inuwar jam’iyyar Labour Party (LP), Mr. Peter Obi, ya bayyana dalilan da suka sanya ba zai bincike gwamnatocin da suka shude ba idan ya zama shugaban ƙasa a 2023.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a birnin tarayya Abuja, yayin da yake amsa tambayoyi jim kaɗan bayan ya bayyana Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed a matsayin mataimakin sa a zaɓen 2023. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya kawo dalilan sa

A cewar sa, zai yi hakan ne domin ya daƙile duk wani abinda zai ɗauke hankalin sa akan mulki sannan kuma domin dakatar da cin hanci.

A dangane da bincikar gwamnatocin da suka gabata, bari na faɗa maka, ni ina akan bakar cewa ba zaka kulle shagon ka sannan ka tafi neman ɓarayi ba. Waɗanda kawai suke kallon jiya da yau zasu rasa gobe. Ubangiji bai bamu idanu a baya ba, ni kawai abinda ke gaba zan kalla

Idan ka shigo gwamnati a yau kace zaka fara dakatar da ɓarna, ƙaruwa za tayi. Ni ba zan kasance cikin duk wani irin takura da tsangwama ba, hakan ba zai faru ba. Dole ƴan Najeriya su rayu akan doka da oda. A cewar Peter Obi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe