27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Ghana: An yi ram da dalilbin da yace minista ya hadu da shugaban kasa da tsamin hammata

LabaraiGhana: An yi ram da dalilbin da yace minista ya hadu da shugaban kasa da tsamin hammata
  • Shugaban TESCON ya ga takansa bayan ya yi wani tsokaci mai kama da tozarci ga ministan yankin arewa na Ghana, Alhaji Sani Ahassan
  • Sayibu Afa Yaba, shugaban TESCON na Jami’ar Fasaha ta Tamale ya yi wata wallafa a Facebook inda yace kamar ministan bai yi wanka ba kafin haduwa da shugaban kasa
  • Wannan dalilin yasa ‘yan sanda su ka nufi har inda yake a ranar Laraba, 10 ga watan Augusta su ka tafi dashi inda babu wanda ya sani.

Shugaban kungiyar dalibai ta NPP na Jami’ar Fasahar Tamale (TESCON), Sayibu Afa Yaba, yana hannun ‘yan sanda kamar yadda Yen.com.gh ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa sun kama shi ne ranar Laraba, 10 ga watan Augustan 2022 bisa zarginsa da yin wani tsokaci mai kama da cin fuska a Facebook ga Ministan yankin Arewa na kasar Ghana, Alhaji Saani Alhassan.

Sayibu ya yi wata wallafa ne a Facebook inda yace alamu na nuna ministan bai yi wanka ba yayin tarbar shugaban kasa Akufo-Addo yayin da ya kai wa yankinsu ziyara.

Kamar yadda GhanaWeb ta ruwaito, Kungiyar Daliban (SRC) ta yi mamakin kamen da aka yi.

“Muna makaranta yau aka kama dan uwan karatun mu. Da farko dai mun yi zaton wasa ne, amma tunda muka ga ‘yan sanda sun sanya masa ankwa mu ka tabbatar da gaske ne,” a cewar shugaban SRC, Dauda Gafaru yayin yi wa Radio Tamale bayani.”

Ya ci gaba da cewa:

“An tambaye mu idan ya dace yadda abokin karatunmu ya yi tsokaci dangane da ministan a Facebook.”

An kama shi ne musamman akan wallafar da yayi a Facebook.

Waɗanda su ka gagara ceto kan su wai su ne za su ceto Najeriya, Ministan Buhari ya ragargaji PDP

Ƙaramin ministan ƙwadago, Mr Festus Keyamo, ya yi shaguɓe ga babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa wato PDP. Ministan yayi wannan shaguɓen ne a wata wallafa da yayi a safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilun 2022.

Ministan Buhari ya soki PDP

Ministan ya ragargaji jam’iyyar akan iƙirarin da ta ke yi cewa za ta ceto ƙasar nan daga halin da ta ke ciki na samun rabuwar kawuna a tsakanin ƙabilun ƙasar.

Jam’iyyar PDP ta daɗe ta na nunawa jam’iyyar APC yatsa kan cewa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin ƙabilun ƙasar nan.

Da ya ke mayar da martani kan zargin da jami’iyyar ta PDP ta daɗe ta na yi, Mr Festus Keyamo ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da hurumin yin wannan zargin ga APC tun ta ƙasa haɗa kawunan ƙabilun da ke cikin ta.

Mr Festus Keyamo ya ce:

Waɗanda ke sukar mu cewa mun raba kawunan ƙabilun Najeriya, sun kasa haɗa kawunan ƙabilun jam’iyyar su; a wajen neman takarar shugaban ƙasa, sun yi nasarar raba kawunan ƙabilun jami’iyyar su. Waɗanda su ka kasa ceto kan su, suna son su ceto Najeriya

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe