Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Tabellah, tayi wuff da kyakkyawan saurayin mijinta, shekara biyar bayan ta tura masa saƙo a shafin Instagram.
Tabeellah da mijinta sun yi aure a watan da ya wuce, shekara biyar bayan sun fara gaisawa a shafin Instgram.
Tabeellah taje kafar sadarwa ta Twitter inda ta bayyana labarin su ita da mijin na ta. Sannan ta kuma sanya hotunan shagalin bikin auren su. Ta dai saka hotunan ne a ranar Laraba 10 ga watan Agusta, 2022.
Yadda alaƙa ta fara a tsakanin su
Dukkanin su dai suna aikin zanen gidaje ne. Labarin su ya fara ne bayan da Tabeellah ta bi wurin tura saƙon kai tsaye ta fara masa magana a shafin na Instagram. Daga nan alaƙa ta ƙullu a tsakani wacce ta zamo silar aure.
Budurwar wacce ta zama matar aure yanzu ta rubuta cewa:
Watan da ya wuce na auri saurayin da na turawa saƙon kai tsaye a shafin Instagram shekara biyar da suka wuce. #Lokacin da ƙauna tayi nasara #Mun haɗu a Instagram #Auren masu zanen gidaje
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
@zakiyagoje ta rubuta:
Ina taya ku murna. Allah Yasa anyi a sa’a, ya baku zaman lafiya.
@yasirAraphat ya rubuta:
Masha Allah, Allah ya sanya albarka ya bada zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba. A ci gaba da neman sa’a.
@ums____ ta rubuta:
Wai kina nufin ke kika fara masa magana? Abin mamaki, Allah yasa albarka a auren ku, Ameen.
@AREMU_IJOHBA ya rubuta
Masha Allah. Allah yasa albarka a ciki. Nima ɗiyar wani ta tura min saƙo, na mu ba zai iya kai shekara biyar ba.
@abbatizakirai ya rubuta:
Masha Allah,haka Allah yake haɗa soyayya muma Allah yasa muga namu saƙon.
Budurwa tayi wuff da mahaifin tsohon saurayin ta, ta bada dalilan ta
A wani labarin na daban kuma wata budurwa tayi wuff da mahaifin tsohon saurayin ta.
Wata budurwa ta auri mahaifin saurayin ta mai shekaru 89 a duniya bayan ta kama saurayin nata yana cin amanar ta.
Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa an saka hoton budurwar mai shekaru 23 a kafar sadarwa ta Instagram. Shafin The Savoy Show shine ya saka hotunan yarinyar a kafar ta Instagram.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com