31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Idan masu mulki suka ci gaba da nuna halin ko in kula tabbas Najeriya zata zama kamar Afghanistan Venezuela, Somalia da Lebanon – Inji  Charly Boy

LabaraiIdan masu mulki suka ci gaba da nuna halin ko in kula tabbas Najeriya zata zama kamar Afghanistan Venezuela, Somalia da Lebanon – Inji  Charly Boy

Shahararren mawaki dan  Najeriya din nan mai suna Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly Boy, ya shiga shafin sa na tuwita domin Jan kunne da gargadin  ‘yan Najeriya.

Najeriya na iya zama kamar Afganistan Somaliya

Da yake magana a ranar Laraba, 10 ga watan Agusta yace, wata kungiya mai suna ‘Area Fada’ ta ce Najeriya na iya zama tamkar  kasashen Afghanistan, Venezuela, Somalia, da Lebanon, idan har mahukuntan kasar suka kasa magance matsalolin da suke cewa  kasar tuwo a kwarya.

najeriya
Idan masu mulki suka ci gaba da nuna halin ko in kula tabbas Najeriya zata zama kamar Afghanistan Venezuela, Somalia and Lebanon

Ya kuma kara Jan hankalin  ’yan Najeriya da su kasance a shirye domin su kare kansu saboda kwararan wasu da ake zargin ‘yan gwagwarmayar fulani ne da aka turo su cikin al’umma  daga wadansu miyagun masu daukar nauyin su domin  ta’addanci. 

Ya wallafa a Twitter cewa wutar rikici ce take ruruwa a Najeriya

“Wata gagarumar  wutar rikici ce take ruruwa  a Najeriya. Ina iya jin hucinta  kuma na kasa cewa uffan. 

Idan mahukunta  da ke kan mulki,  sun kasance masu halin ko in kula,  ko kuma suka  kasa gyara matsalar wannan badakalar da ake ciki, to tabbas Najeriya zata zama a yanayi irin na kasashen  Afghanistan,  Venezuela, Somalia da Lebanon.

Fulani masu fafutuka zasu iya kawo hari a kowanne lokaci

Ya kara da cewa, an saki wasu da suke ikirarin fafutukar kwato Halkin fulani, wato Fulani Freedom Fighters (FFFs) domin aiwatar da ta’addanci, saboda haka, ‘yan Najeriya ku shirya domin kare kan ku”

A kwanakin baya, Charly Boy din  ya ce zai bar Najeriya zuwa kasar Ghana idan Tinubu ko Atiku Abubakar suka lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2023.

Yadda ‘yan Afganistan ke siyar da kodarsu saboda tsananin yunwa da talauci

Rashin aikin yi, bashi, da rashin abinda zai ciyar da ’ya’yansa a Afganistan, shi ya sa Nooruddin ya yanke shawarar siyar da kodarsa – yawan’ yan kasar Afganistan da ke sayar da kodan su yana karuwa don kawai su ceto iyalan su daga matsin rayuwa.

Wannan dabi’ar abu ne da ya zama ruwan dare kuma gama-gari a yammacin birnin Herat da ke Afganistan har ta kai ga an yi wa wani kauye lakabi da “kauyen masu koda daya”.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe