37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Dalilin da yasa na fassara Al-Qur’ani mai girma zuwa harshen Igbo -Malam Murtala Chuwkuemeka

IlimiDalilin da yasa na fassara Al-Qur'ani mai girma zuwa harshen Igbo -Malam Murtala Chuwkuemeka

Malam Muhammad Murtala Chuwkuemeka ya zama abin magana bayan ƙaddamar da fassarar Al-qur’ani cikin harshen Igbo da yayi wanda ya fara aikin sa shekara biyar da suka gabata.

Ɗan asalin jihar Imo wanda ya musulunta shekara 33 da suka wuce ya bayyana cewa ya fassara ayoyi 6,236 na Al-Qur’ani mai girma.

Ya bayyana dalilan sa

A wata da hira tashar BBC News Pidgin, Chuwkuemeka ya bayyana cewa yayi hakan ne domin yana son Inyamurai su san addinin musulunci. Jaridar Legit.ng ta rahoto

Ya bayyana cewa: 

Na fassara Al-Qur’ani zuwa harshen Igbo domin ina son Inyamurai su san addinin musulunci don suna kiran shi a matsayin addinin Hausawa, Yarbawa da Larabawa

Ba su yarda cewa musulunci na kowa bane. Akwai Al-Qur’ani na Hausa, Al-Qur’ani na Yarbanci, Al-Qur’ani na Turanci amma babu na yaren Igbo kafin yanzu.

Ya samu yabawa sosai daga Hausawa da Yarbawa

Malamin yace ya samu yabawa sosai daga Hausawa da Yarbawa fiye da Inyamurai

Wasu Hausawa da Yarbawa da suka karanta fassarar Al-Qur’ani na zuwa harshen Igbo sun ji daɗi matuƙa

A gaskiya, sun ji daɗi sosai fiye da ƴan’uwana Inyamurai. Wasu daga cikin su sun ce za suyi amfani da Al-Qur’anin su koyi yaren Igbo.

Ya nuna godiyar sa ga al’ummar musulmai

Yayin da yake bayyana cewa Suratul Baqarah itace Surar da tafi tsawo a littafi mai tsarki da ya fassara, ya fassara ta cikin shekara biyu. Chukwuemeka ya godewa al’ummar musulmai bisa taimakawa wurin samun nasarar da yayi.

Da al’ummar musulmai ba su ƙarbeni a matsayin Inyamuri ba, da ban samu nasarar fassara Al-Qur’ani ba.

Kungiyar Musulmai yankin kudu Za ta Kaddamar da Al-Qur’ani Mai Girma da aka Fassara Zuwa Harshen Ibo ranar Juma’a

A wani labarin kuma za a ƙaddamar da Al-Qur’ani mai girma da aka fassara zuwa harshen Igbo.

Wakilan kungiyar da ke karkashin kungiyar Da’awah Muslim Ibo karkashin jagorancin Mal. Muhammed Murtala Chukwuemeka ya bayyana hakan ne a jiya a yayin wata ziyarar ban girma da ya kai ofishin Daily Trust a Abuja.
Da yake jawabi yayin ziyarar.

Chukwuemeka ya ce shi da tawagarsa sun yanke shawarar isar da sakon Allah ga ‘yan’uwansu Igbo ta hanyar fassara Qur’ani zuwa yaren su.

Mal. Chukwuemeka, dan asalin karamar hukumar Orlu ta jihar Imo, ya bayyana addinin musulunci a matsayin addinin zaman lafiya da ya haramta kashe mutane

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe