27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Ƴan bindiga sun sake afkawa iyalan Ango Abdullahi, sun sace sirikar sa da ƴaƴanta

LabaraiƳan bindiga sun sake afkawa iyalan Ango Abdullahi, sun sace sirikar sa da ƴaƴanta

Ƴan bindiga sun sake sace sirikar shugaban ƙungiyar dattawan Arewa, Ango Abdullahi, wata ɗaya bayan an sako Sadiq, ɗaya daga cikin ƴaƴan sa.

Ango Abdullahi ya tabbatar da aukuwar lamarin

Ango Abdullahi ya tabbatar da aukuwar hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Laraba, inda yake cewa an kuma tafi da yaran ta guda huɗu.

Sirikata Ramatu Samaila, na daga cikin mutanen da aka sace tare da yaran ta guda huɗu. Matar sirikina ce wansa shine magajin garin Yakawada. Inji shi.

Majiyoyi sun tabbatarwa da Daily Trust cewa ƴan bindigan sun shiga ƙauyen Yakawada a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a daren ranar Talata inda suka afka gidan magajin garin, Alhaji Rilwanu Saidu.

Sun kuma yi awon gaba da iyalan makwabcin magajin garin

Daily Trust ta tattaro cewa bayan sun sace iyalan magajin garin, sun kuma sace wasu mutane a cikin makwabtan sa.

Sun kuma shiga gidan makwabcin magajin garin, inda suka sace mai gidan, Abubakar Mijinyawa tare da matan sa biyu, Aisha da Hajara. Matan guda biyu dukkan su shawarya suke inda aka tafi da su tare da jariran su.

Majiyoyin sun cigaba da cewa ƴan bindigan sun halaka wani mai gadi, Aminu Lawal a yayin harin.

Mutum uku da suka samu raunuka a yayin harin, na amsar magani a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Saɗiq Ango Abdullahi yana daga cikin mutanen da aka sace a harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a watan Maris. An sako shi bayan watanni huɗu a tsare.

Ƴan bindiga sun sace Hakimi, ƴan ƙasar waje 2 da mutane 9 a jihar Zamfara

A wani labarin na daban kuma ƴan bindiga sun sace Hakimi da ƴan ƙasar waje 2 ada wasu mutane a jihar Zamfara.

Ƴan bindiga sun sace Hakimi, ƴan ƙasar waje 2 da mutane 9 a jihar Zamfara.

Ƙasa da kwanaki bakwai bayan ƴan bindiga sun ƙona kauyuka biyar a wani mummunan harin da suka kashe aƙalla mutane 200, yan bindigan sun ƙara ɗauke mutane 12 a wani sabon harin da su ka kai a jihar Zamfara

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe