37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yadda Dangote yayi ƙasa cikin jerin attajiran duniya, ya rasa N360bn cikin sa’o’i 8

LabaraiYadda Dangote yayi ƙasa cikin jerin attajiran duniya, ya rasa N360bn cikin sa'o'i 8

A ranar Talata 9 ga watan Agusta, 2022, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ga an kwashe N360bn  ($863m) na dukiyar sa cikin sa’o’i 8 na cinikayya.

A cewar Bloomberg Billionaires Index, wanda yake jerin manyan attajirai 500 na duniya, dukiyar Dangote yanzu tayi ƙasa $19bn saɓanin sama da $20bn da take a watan Mayun 2022. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Ya dawo na 80 cikin jerin attajiran duniya

Ƙiyasin adadin dukiyar Dangote na yanzu ya sanya ya zama mutum na 80 mafi arziƙi a duniya, inda ya faɗo daga na 60 da yake a cikin watanni biyu kawai da suka wuce.

Dukiyar Dangote dai ta fi ƙarfi a kamfanin simintin sa inda yake zaman wanda yafi kowa hannun jari.

Dalilin da yasa dukiyar sa ta ragu

A ranar Talata 9 ga watan Agusta, farashin hannun jarin simintin Dangote a kasuwar hannun jari da kaso 9.05 inda ya ƙare a N241 daga N265 da ya aka fara da shi a ranar Litinin.

Bayanin Bloomberg kan dukiyar attajirin yace:

Mafi yawan arziƙin Dangote yana samuwa ne daga kaso 86 na hannun jarin sa a kamfanin simintin sa. Yana riƙe da hannun jarin ne ta hannun rukunin kamfanunnikan sa.

Kadarar sa ta biyu mafi daraja kamfanin taki ne mai samar da ton miliyan 2.8 na uriya a shekara, a cewar kamfanin dillancin labarai na duniya.

Matatar man fetur ta kuɗi $12bn wacce ake aikin ginin ta a Najeriya ba a sakata a cikin darajar kadarorin sa domin bata fara aiki ba kuma kuɗin gina ta anyi hasashen za su fi darajar ta a yanzu.

Duk da arziƙin sa ya ƙaru, Dangote ya koma baya a cikin jerin attajiran duniya

A wani labarin kuma, Dangote yayi ƙasa cikin attajiran duniya duk da ƙaruwar dukiyar sa.

Duk da ƙarin arziƙin da ya samu a dalilin neman da ake yiwa simintin sa, wanda yafi kowa arziƙi a nahiyar Afrika, Aliko Dangote, ya faɗo ƙasa daga matsayin sa na mutum na 60 a cikin jerin attajiran duniya.

Jaridar Legit.ng ta samo cewa dukiyar sa ta ƙaru da fiye da $1.7bn a wannan shekarar, inda arziƙin sa ya kai $20.2bn a watan Yunin 2022, saboda ƙarin daraja da kamfanin simintin sa ya samu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe