27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Tsarin Ponzi: NDIC ta gargadi ‘yan Najeriya kan cibiyoyin kudi na yaudara

LabaraiTsarin Ponzi: NDIC ta gargadi 'yan Najeriya kan cibiyoyin kudi na yaudara

p

NDIC

Hukumar Inshorar Deposit Insurance Corporation (NDIC), ta shawarci ‘yan Najeriya da su yi hattara da tsare-tsaren ponzi da ke aiki a karkashin inuwar cibiyoyin kudi.

Cibiyoyin kudi na yaudara

Shugaban shiyya na NDIC, shiyyar Ilorin, Chima Onyechere, wanda ya bayar da shawarar a ranar Laraba a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya ce irin wadannan cibiyoyin kudi sun kasance na damfara ne.

An yi gangamin wayar da kai

Mista Onyechere ya ce, kamfanin ta yi gangamin wayar da kan jama’a a fadin kasar nan, tare da gargadin masu damfara da ke gudanar da ayyukan ponzi.

Akwai masu amfani da ponzi da yawa a duk fadin kasar nan, musamman a karkara. Mutane a waɗannan wuraren ƙila ba za su san makircinsu ba saboda suna yaudarar mutane da irin riban da ake samu masu yawan.
“Suna yaudarar mutane su sanya kudi a cikin cibiyoyin hada-hadar kudi na bogi su kuma mutane ba su san cewa ba bisa ka’ida ba ne.

Don haka ne NDIC ke isar da sako ga kowa da kowa kan bukatar neman cibiyoyin hada-hadar kudi wadanda ke da takardar shedar gudanar da aiki.
“Duk lokacin da ‘yan Najeriya suka ci karo da wadannan cibiyoyin kudi ba tare da takardar shaidar NDIC ba, ya kamata su yi tambayoyi don gano ko suna da inshora a karkashin NDIC kafin yin wani kasuwanci da su,” i
nji shi.
A cewar Onyechere, ana sanya lambobi NDIC a kan cibiyoyin hada-hadar kudi kamar bankunan da kamfani ke ba da inshora da kuma tabbatar da amincin yin kasuwanci.

Hukumar KAROTA tayi babban kamu, ta cafke babbar mota maƙare da giya a jihar Kano

Hukumar KAROTA ta jihar Kano, ta samu nasarar tare wata motar dakon ƙaya maƙare da giya wacce takai darajar maƙudan kuɗaɗe har N50m.

Kakakin hukumar, Nabilusi Abubakar, ya bayyana cewa giyar takai kiret 2000 a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 28 ga watan Yulin 2022. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

An karrama jami’in da kyautar kudi
Babban darektan gudanarwa na hukumar, Hon. Baffa Babba Dan Agundi, wanda ya tabbatar da kamen ya kuma ba jami’in da ya tare motar tukwuicin N1m saboda ƙin karɓar cin hancin N500,000 domin ya saki kayan.

A cewar sa gwamnatin jihar ta haramta shigowa da shan giya a ilahirin jihar, sannan hukumar sa ba zata saurarawa duk wanda ta samo na shigowa da irin waɗannan kayan mayen cikin jihar.
Ya yabawa zaƙaƙurin jami’in sannan kuma ya nemi sauran jami’an hukumar da suyi koyi da shi sannan su riƙa la’akari da lafiya da dukiyoyin mutane sannan da jindaɗin jihar kafin wani abu daban.

Tsoron Allah yasa naƙi karɓar cin hancin
Halilu Kawo Jalo, jami’in da ya cafke kayan yace an cafke kayan tare da taimakon masu bada bayanai waɗanda suka sanar da su dangane da kayan.

Mun tare motocin dakon kayan a kan titin Obasanjo suna hanyar zuwa Sabon Gari na jihar. Sun bani cin hanci amma naƙi karɓa saboda na san illar da giya ke haifarwa ga rayuka. Haramun ce sannan kuma ya saɓawa koyarwar addinin musulunci ƙarbar cin hanci, hakan ya sanya nayi abinda ya dace.
Baffa ya kuma yi kira ga al’umma da su goyi bayan hukumar sa domin tsaro da kuma lafiyar jihar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe