24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Yadda likita ya mayar wa mata wuya kamar jikin kadangare daga zuwa a matse mata fata

LabaraiYadda likita ya mayar wa mata wuya kamar jikin kadangare daga zuwa a matse mata fata

Jayne Bowman, mai shekaru 59, daga Hampshire, ta biya £500 ga likitoci don su yi mata aiki (fibroblast) wanda zai sa a matse mata fatar wuyanta, LIB ta ruwaito.

Yayin aikin, an sanya mata wata na’urar lantarki mai karfi wacce zata dinga ratsa fatarta don gyaran.

Sai dai aikin wata likitar inganta halitta da Jayne ta hadu da ita a manhajar Facebook ta bar ta da tabbai jajaye da yawa.

Yayin da tabban ke bata, Jayne ta yada labarin nata ne don jama’a su kula da aikata irin wadannan abubuwa.

Kakakin bangaren kula da lafiya ya bukaci idan mutum na son yin gyare-gyare ya nemi kwararrun likitoci da su ka san abinda su ke yi a bangaren.

A cewar Jayne:


“Bana fita waje idan ban boye wuyana da kyalle ba. Hasali ma na tsani fita, na gwammaci in fita idan ana ruwa yadda babu wanda zai kula da ni.

“Ba na yi wa likitoci masu gyarar sura kudin goro bane, amma dayawansu basu san abinda su ke yi ba. Idan za ka yi gyara ka nemi kwarru.”

Jayne ya bayyana yadda a tunaninta bayan kula da abincin da take ci za ta yi kyau, amma sai ga kuncinta ya rabu gida biyu.

Ta ci gaba da cewa:

“Ina ta jindadin yadda na rage kiba amma sai ga shi fata ta ta tattare wuri guda inda kunci na yayi muni, ban son hakan.”

Yadda ‘yar Najeriya ta sheka lahira bayan garzayawa gaban likita don kara girman mazaunanta

Wata ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna poshcupcake_1, cikin alhini ta bayyana yadda kawarta, Crystabel ta mutu bayan yunkurin kara girman mazaunanta da ta yi, Prewedding Nigeria ta ruwaito.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta tare da sanya hotunan mamaciyar:

“Ina son sanar da jama’a cewa wata kawara ta rasu a wannan asibitin da ke Jihar Legas, kwanaki kadan da su ka gabata bayan ta je a yi mata aiki.

“Ba wai ina shawartar kowa da ya ki zuwa a inganta masa surar jikinsa ba ne, ka yi idan kana so.

“Amma ina shawartarka da ka kiyaye zuwa wurin likitocin da ke ikirarin sun samu gogewa a kasar waje, su zo Najeriya su dinga halaka matasa.

“Bayan gama aikin, ta sanar da likitan yadda ya ke ta zubar da jini. Amma a haka ya ce babu komai zai tsaya.”

Ta ci gaba da kalubalantar iya aikinsa inda ta ce bai damu ba ko da kawarta ta bayyana masa cewa tana ta zubar da jini.

Ta ce abin ban takaicin shi ne yadda ta rasu ba tare da sanar da wani kowa a gidansu halin da ta ke ciki ba. Sai wasu kawayenta da su ka san ta yi aikin ne su ka bibiyeta daga nan aka ba su takarda cewa gawarta tana ma’adana gawa.

Ta bukaci gwamnati ta sanya ido akan likitocin bogi ta kuma kama duk wasu marasa gogewa a fannin tare da kwace lasisin aikinsu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe