24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Ni ne a bidiyon da aka kama ‘yan luwadi, amma zan yi karin bayani, Yahaya Shareef

LabaraiNi ne a bidiyon da aka kama ‘yan luwadi, amma zan yi karin bayani, Yahaya Shareef

Wani fitaccen dan TikTok da Instagram, Yahaya Shareef ya bayyana cewa shi ne a cikin wani bidiyo wanda ake ta yadawa wanda ‘yan sanda su ka titsiye ‘yan luwadi a Jihar Kano, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Matashin wanda ya samu shahara a kafafen sada zumuntar zamani ya dade yana daukar hankalin jama’a tun daga kyawun siffarsa da kuma iya sanya suttura.

yahaya
Ni ne a bidiyon da aka kama ‘yan luwadi, amma zan yi karin bayani, Yahaya Shareef

Har ila yau, ana ganin hotuna da bidiyonsa a Dubai, Saudi Arabia da sauran kasashe, wani lokacin ma har tare da ‘yan uwansa da mahaifiyarsa.

Ana ganinsa yana rike da tsadaddun wayoyi a cikin falo da dakuna na alfarma inda yake hawa kan wakoki tare da kwasar rawa.

Sai dai kwatsam sai ga wani bidiyo ya bayyana wanda ‘yan sanda su ka titsiye shi a matsayin daya daga cikin wadanda ake zarginsu da aikata luwadi da damfara.

Ganin bidiyon ya fara bazuwa ne yayin da wasu ke cewa shi ne wasu kuma su na musantawa yasa ya fito fili ya bayyana gaskyar abinda ya sani.

A cewarsa, tabbas shi ne a cikin bidiyon amma idan jama’a sun kula dakyau bai amsa laifin yin luwadi ko kuma damfarar kowa ba.

Ya ce ko a lokacin ‘yan sanda ne su ka tasa shi gaba inda su ka tilasta masa amsa laifin da bai aikata ba. Amma kuma lokaci ya yi da zai yi bayani dalla-dalla.

A cewarsa, shekaru 4 kenan da faruwar lamarin kuma wasu ne su ka shirya hakan musamman don tozarta shi, amma a lokacin da yayi bidiyon yana wani aiki ne, daga baya zai natsu ya fallasa sunaye.

Ya ce Allah ya rufa masa asiri don kasuwancinsa yake yi. Idan akwai wanda ya san ya neme shi, ya fito ya bayyana wa duniya.

Hukumar kasar Saudiyya sun kama kayan ‘yan luwadi da madigo da aka shiga da su kasar

Hukumar kasar Saudiyya ta cafke wadansu kayan roba da ake amfani dasu wajen yin madigo, da kuma kayan sakawa da ake zargin ‘yan kungiyar luwadi da madigo ne zasu yi amfani da su. 

Ma’aikatar ciniki ta kafa tawagar amsu binciken irin kayan

Ma’aikatar ciniki, ita ce ta wakilta wadansu jami’ai da zasu dinga bincike da sa ido wajen ganin an binciko irin wadannan kaya, inda kuma suka yi nasarar binciko kayan, wadanda suke sanya matasa da yawa shiga aikata ayyukan madigo da luwadi. 

Wadannan kaya babu shakka suna sanya karin yaduwar fasadin madigo da luwadi, wanda kuma mai binciken ya shaida cewa, ana shigo da su ne saboda matasa mata da maza. 

Nau’in kayan luwadi da madigo  da aka bankado

Kayan sun hada da mazakuta ta roba da wasu kaya na sakawa a jiki, wadanda suke da alaka da kungiyar nan ta mata ‘yan madigo, wato LGBT. 

Haka kuma, shima mai sayarwa wanda aka kama kayan a kantin sa, ya musanta cewa kayan na yan luwadi da madigo ne, inda ya nuna cewa, kawai an sami arashi ne na launin kayan nasa da kuma launin tutar kungiyar ta yan madigo, wanda duk launin su shine launin bakan gizo. 

Matsayin hukuncin laifin

Luwadi da madigo dai ba laifi bane a kasashen turawa, amma babban laifi ne kuma haramun, a addinin musulunci. 

Farmakin bazata, aikine na ma’aikatar ta kasuwanci, dalilin da yasa suke aiwatar da samame , shago-shago domin su kama irin wadannan kaya kuma su tabbatar ba’a shigo da abin da zai gurbata tarbiyyar al’umma ba, gami da tabbatarda bin dokar kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe