27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

An yi wa wani gwamna a Arewa ihu barawo 

LabaraiAn yi wa wani gwamna a Arewa ihu barawo 

Daruruwan ‘yan jam’iyyar APC sun muzanta  gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq. 

Abin da ya ja aka yi ma gwamnan ihu barawo

Jaridar POLITICS NIGERIA,  ta samu labarin cewa fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar APC, su na shirin sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Amma yayin da Gwamna Abdurrazzaq din ya yi ƙoƙarin shiga tsakani, sai suka kore shi  inda suka dinga  rera taken  “Ole” ma’ana, “barawo” da kuma “Sai Bukky”. 

Taken “Sai Bukky” wani take da ‘yan siyasar jihar Kwara ke yi domin jinjina ga Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar, kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Jijar Kwara tana fama da rikicin cikin gida a APC

Jihar Kwara na daya daga cikin jihohin da ake ganin rikicin cikin gida na barazana ga jam’iyyar APC mai mulki a daidai lokacin da zaben shekarar  2023 ke kara gabatowa.

A hasashen masana, idan dai har ba’a hakurkurtar da fusatattun  yan jamiyyar ba, to jihar ta Kwara,  na iya fuskantar yanayi irin na jihar Osun.

Gwanatin jihar Kwara ta rushe ginin Bukola Saraki duk da hukuncin kotu

Duk da hukuncin da kotu tayi akan ginin Olusola Saraki, wanda aka fi sani da Ile Arugbo, gwamnatin jihar Kwara ta sa an rushe ginin.

An yi rusau din a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairu, bayan wata bulldozer wacce mallakin gwamnati ce ta isa wurin da misalin 2:25am zuwa 4:20 ta rushe ginin.

Kafin rusau din babbar kotun jihar Kwara ta yi hukunci akan ginin wanda kamfanin Asa Investment Ltd ya kai korafi akai.

Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa 17 ga watan Maris don karasa hukunci. Saraki ya hassala akan yadda gwamnati ta rushe ginin, inda yace gwamnati tayi zalunci tunda har yanzu ba a kammala shari’ar ba.

Akin Onigbinde (SAN), babban lauyan Asa Investment Ltd, ya ce gwamnati bata kyauta ba da ta rushe ginin ba tare da umarnin kotu ba.

A wani labari na daban, alkalin babbar kotun jihar Delta, Anthony Okorodas, ya ce bai dade da gano cewa yara 3 da ya haifa da tsohuwar matarsa duk ba yaransa bane.

Ya bayyana yadda wannan lamarin ya bashi mamaki kuma ya firgitar dashi don har ya dauki nauyin 2 daga cikinsu yanzu haka suna karatu a jami’a sannan karaminsu shekarunsa 17.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe