27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Saudiyya ta sanar da muhimman sabbin sauye-sauye kan aikin Umrah

LabaraiSaudiyya ta sanar da muhimman sabbin sauye-sauye kan aikin Umrah

Sabon lokacin fara aikin Umrah ya shiga a cikin satin da ya gabata. A wannan shekarar masu yin Umrah daga ƙasar waje za su iya shigowa Saudiyya su gudanar da aikin Umrah ba tare da an ƙayyade adadin lokacin gudanar da ita ba.

Sabbin sauye-sauyen da aka kawo kan masu son yin Umrah

A cewar wani gidan labarai na Saudiyya, Ajel, ministirin Hajji da Umrah tace, musulmai ƴan ƙasashen waje za su iya shiga da fita Saudiyya a kowace tashar jirgin sama ba lallai sai tashar jirgin sama ta birnin Jeddah ba. Jaridar Islamicinformation ta rahoto.

Dole ne masu son yin Umrah su amshi izni daga manhajar ‘Eatmarna’ idan har ba su ɗauke da wata cuta ko kuma ba su haɗu da wani mara lafiya mai ɗauke da cuta ba.

Idan aka shiga cikin manhajar, musulman da suka fito daga ƙasashen waje za su samu damar tsara irin abincin da suke son ci ba tare da taimakon wani ba.

Ɗaukar wannan matakin zai tabbatar cewa Alhazai sun samu abubuwan da suka dace kuma hakan zai ƙara musu armashin tafiyar su.

Daga cikin ƙoƙarin sauƙaƙa samun damar yin abubuwa ga Alhazai, mutanen da suka fito daga ƙasashen waje za su iya tanadar dabinon su a manhajar ‘Eatmarna’ da zaran sun karɓi iznin shiga ƙasar.

An bayyana adadin mutanen da ake sa ran za su yi Umrah a wannan shekarar

Bisa la’akari da shekarar musulunci, sabon lokacin fara aikin Umrah ya fara ne a ranar 30 ga watan Yuli, 2022, wacce ta zo daidai da ranar farko a shekarar musulunci (Hijri).

Ana sa ran cewa sama da mutum miliyan 10 ne za su yi aikin Umrah a bana a Saudiyya, a cewar hukumomi.

Wani mutumi dan asalin kasar Iraqi ya isa Saudiya bayan shafe watanni 11 yana tafiya a ƙafa domin sauke farali a hajjin bana

A wani labarin kuma, wani mutumi ya isa Saudiyya bayan shafe watanni 11 yana tattaki a ƙafa domin sauke farali. Mutumin dai ɗan ƙasar Iraqi ne kuma ya isa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.

Wani dan kasar Iraqi, mai suna Adam Muhammad wanda ya isa birnin Makkah da kafarsa, inda kafin isar sa sai da ya ratsa kasashe 11, tare da kwashe kimanin watanni 11 yana tafiya domin isa kasa mai tsarkin don sauke farali a hajjin bana.

Adam Muhammad wanda ya dade yana mafarkin ganin yakai ziyara kasa mai tsarki da kafar sa, abun da mutane da dama suke ganin abu ne da kamar wuya kasancewarsa mazaunin kasar Burtaniya, bayan isar sa kasa mai tsarki, ya yi umrah, ya kuma shafe lokaci mai tsawo a Ka’aba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe