31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Ma’nene: Jama’a na tono gawawwakin ‘yan uwansu don wankesu, kayatasu da daukar hotuna tare

LabaraiMa’nene: Jama’a na tono gawawwakin ‘yan uwansu don wankesu, kayatasu da daukar hotuna tare

A ko wanne yanki akwai tasu al’adar wacce su kan yi don tunawa da ‘yan uwansu da su ka mutu, amma mutanen yankin Tana Toraja, yadda su ke nasu na da bambanci da na sauran jama’a, Insidegistblog ta ruwaito.

Shagalin Ma’nene su ke yi, wanda biki ne na musamman don bautar matattun da su ka rigaye su.

Idan mutum ya mutu a yankin, ana wanke gawarsa sai a birne shi a cikin dutse. Ta wannan hanyar ne ake adana gawar mamata yadda ‘yan uwansu za su iya tono ta lafiya lau.

Mutanen Torajan cike da alfahari su ke nuna matattun ‘yan uwansu bayan hako su daga inda aka birne su sannan su sanya musu tufafi masu kyau, duk a matsayin hanyar nuna kauna ga mamatan.

Har hotuna su ke yi da gawawwakin

Duk shekara, mutanen Toraja daga Tsibirin Sulawesi su na kai wa kaburburan mamatansu ziyara din su tono su sannan su wanke gawarsu tare da sanya mata sabbin tufafi don daukar hotuna.

Ana kiran wannan shagalin da Ma’nene. Duk da dai cocinan Toraja da dama sun so kawo karshen wannan al’ada, amma abin ya gama ratsa mutanen Torajan.

Gwamnatin Indonesia kanta ta san da wannan al’adar mara tsari.

Wani mutum ya kashe ‘ya’yansa mata 3, ya jefa gawawwakin a cikin firij – ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya ta kama wani mutum bisa zargin kashe ‘ya’yansa mata uku.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya ta kama wani mutum bisa zargin kashe ‘ya’yansa mata uku.

Babba a cikin yaran tana da shekaru 11, yayin da ƙaramar ta kasance ‘yar shekara hudu. Dayar kuma ‘yar shekara takwas ce, , a cewar ‘yan sandan.

Mutumin mai suna Ifeanyi Amadikwa mai shekaru 52 ya jefa gawarwakin yaran a cikin firji, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe ya bayyana a wata sanarwa a ranar Laraba. Mista Amadikwa, wanda ke zaune a lamba 74 Nkwubor Road, Emene, kusa da Enugu, an kama shi ne a ranar 4 ga watan Janairu da misalin karfe 7:30 na dare. Bincike na farko ya nuna cewa matar wanda ake zargin kuma mahaifiyar yaran sun je kasuwa da danta daya tilo a ranar 4 ga watan Janairu, inda suka bar sauran a hannun wanda ake zargin.

Da ta dawo da yammacin ranar da aka ce, kuma ba ta sami ko ɗaya daga cikin yaran uku ba. “Amma yayin da ake neman su, wadda ake zargin ya ja hankalinta kan firjin da ya dawo da shi gida daga shagonsa a ranar 2 ga watan Janairu kuma ya ajiye a barandar gidansu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe