31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Kololuwar wayewa: Har yanzu ban gama ba, Mutumin da yayi gyare-gyare fiye da 516 a jikinsa

LabaraiKololuwar wayewa: Har yanzu ban gama ba, Mutumin da yayi gyare-gyare fiye da 516 a jikinsa

Wani mutum dan kasar Jamus ya kafa tarihi a littafin tarihin duniya na Guinness inda ya kasance mutumin da ya fi kowa sauya halittarsa a duniya, ndtv.com ta ruwaito.

Rolf Buchholz ya yi sauye-sauye fiye da 516 a jikinsa kuma ya ce har yanzu bai kammala ba kamar yadda UPI ta ruwaito.

Kamar yadda rahoton littafin tarihin duniya na Guinness ya bayyana, Rolf yana aiki ne da wani kamfani na fasahar labarai da ke Jamus.

Sai da ya kai shekaru 40 da haihuwa sannan ya fara sauye-sauyen a jikinsa inda aka dinga yi masa zane da kuma huje-huje iri-iri.

Tun bayan nan da fiye da shekaru 20, ya sauya gaba daya kasancewar an yi masa huje-huje a lebe, gira, da hanci sannan kuma an yi masa kananun kahonni biyu a goshinsa.

“Sauye-sayen da nayi, jikina kadai su ka sauya, ba su sauya halaye na ba,” a cewar Rolf.

A cikin sauye-sauyen akwai huje-huje fiye da 453, zane-zane a jikinsa da sauransu. A shekarar 2010 ne ya kafa tarihin littafin Guinness a matsayin mutumin da ya fi kowa huji a jikinsa.

Ya dauki hankalin jama’a ne a hanyarsa ta dawowa daga Dubai a filin jirgin sama a 2014, inda ya isa yana neman masauki.

Kakakin otal din inda Roff Buchholz ya so sauka ya ce babu yadda bai yi ba amma ba a bar shi ya shiga otal din ba.

Bayan shekaru 5 da yin wadannan sauye-sauyen ne Rolf ya je aka yi masa kahonni a goshinsa. Hankali ya kara komawa kansa bayan littafin rahotannin duniya na Guinness ya bayyana bidiyonsa a shafinsu na kafar sada zumunta.

Dan Afirka ya kafa tarihi, shi ne mutumin da yafi kowa wangamemen baki a duniya

A tarihin ana samun mutumin da ya fi kowa kyau, gajarta, tsayi, ilimi, kwakwalwa, iya ado da sauransu, amma a wannan karon Francisco Domingo Joaquim shi ne mutumin da ya fi kowa girman baki a duniya, Instablog9ja ta ruwaito.

Francisco Domingo Joaquim shi ne dan nahiyar Afirka daga kasar Angola wanda ya kafa babban tarihin a duniya.

Kamar yadda aka tabbatar, gaba daya gwangwanin lemu ya na iya shiga bakinsa ya kuma boye tsaf kamar yadda hotonni su ka bayyana.

A shekarar 2010 masu bincike sun gano yadda Francisco Domingo Joaquim, mai shekaru 28 da haihuwa ya kasance mutumin da yafi kowa katon baki a duniya.

Fadin bakinsa ya kai inci shida da rabi (6.5inches), sannan gwangwani mai girman 330ml yana iya shiga bakinsa, kamar yadda littafin tarihin duniya na Guinness ya bayyana.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe