34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Mun Kama wadanda suke da hannu a Harin Cocin Owo – Janar Irabor

IlimiMun Kama wadanda suke da hannu a Harin Cocin Owo - Janar Irabor
irabor.jpeg

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar kama wadanda ake zargi da kashe masu ibada a St. Francis Catholic.
Da yake magana a wani taro da editoci da shugabannin kafafen yada labarai a Abuja ranar Talata, Irabor ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargi bayan kammala bincike.
A cewarsa, sojojin sun kashe ‘yan bindiga da dama da ke ta’addanci a kasar.
Ya ce, “Bari in sanar muku an samu munanan ayyuka na ’yan iskan gari wadanda suka kawo mana cikas ga rayuwarmu baki daya, kamar harin jirgin kasa, harin da aka kai gidan yarin Kuje,da kuma harin da aka kai kan ayarin motocin shugaban kasa.
“Har ila yau, harin Owo wanda aka yi an taba maza da mata wanda hakan sai ya zama kamar cewa al’ummar kasar na cikin wani mawuyacin hali. Mun kama wadanda suke da hannu a wannan aika aika a Owo
.”
Labarun hausa ta ruwaito yadda ‘yan ta’adda a ranar 5 ga watan Yuni 2022 suka kai hari cocin St. Francis Catholic Church, Owo, Jihar Ondo, tare da kashe masu ibada da dama.

An kashe shugaban ‘yan ta’adda da matansa a harin da jirgin sama ya kai jihar Katsina

Rundunar sojin saman Najeriya, ta kai wani samame da safiyar Lahadi, inda ta yi nasarar kashe shugaban kungiyar ‘yan ta’adda da ke aiki a Zamfara, Abdulkarimu Faca-Faca tare da matansa biyu da manyan kwamandojin sa takwas.
An kai farmakin ta sama ne da misalin karfe 3 na safiyar Lahadi a kauyen su mai suna Marina, a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
PREMIUM TIMES ta tattaro bayanai daga wata majiya da ke sansanin ‘Forward Operation Base (FOB)’ da ke Katsina cewa an kai harin ne bayan da jami’ansu suka samu rahoton sirri kan inda Mista Faca-Faca yake.
Kakakin hukumar ta FOB, Abdul Olaitan, bai amsa tambayoyin da aka aike masa ba game da harin, amma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isa ya tabbatar da cewa an kai harin bam a gidan shugaban kungiyar.
An kashe ‘yan ta’adda takwas da ake zargin ‘yan ta’adda ne da suka hada da shugabansu Abdulkarim Faca-Faca a farmakin da NAF ta kai a jiya, kuma da safiyar yau a wannan yanki domin gudanar da aikin kawar da ‘yan ta’adda ,‘yan ta’addan sun gudu amma duk shanunsu sun halaka yayin da da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga. Rahotanni ya tabbatar da hakan, ”in ji Mista Isa a cikin sakon WhatsApp.
Dan majalisar mai wakiltar Safana a majalisar dokokin jihar Katsina, AbdulJalal Runka, shi ma ya tabbatar da harin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe