31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Jarumin Maza: Mutumin da yake da Mata 15 da ‘ya’ya 107 , Ya Ce Ya fi karfin Wayon Mace Daya

LabaraiJarumin Maza: Mutumin da yake da Mata 15 da ‘ya’ya 107 , Ya Ce Ya fi karfin Wayon Mace Daya
826179fb5f123896

Wani dattijo mai shekaru 61 mai suna David Sakayo Kaluhana mai mata 15 da ‘ya’ya 107 ya yadu a yanar gizo inda ya haifar da ce-ce-ku-ce.David ya shaidawa Afrimax a wata hira da aka yi da shi cewa yana da niyan karo wasu matan ya ce maza masu mata daya rashin wayau ne.

Kai na yafi karfin mace daya

A cewarsa, yace ya fi karfin wayaun mace daya shi ya sa yake da tarin iyali.
Kai irin nawa mace ɗaya ta yi min kadan saboda girman sa.
“Shi yasa na auri mata da yawa don na fi karfin wayau mace daya.”

Daya daga cikin matan David ta yi magana

Jessica Kaluhana, daya daga cikin matan David ta yaba mijin a hiran su da Afrimax. Jessica ta ce ta auri David ne a shekarar 1998 kuma ta haifi ‘ya’ya 13 da shi, yayin da 11 daga cikinsu ke ne kawai ke raye.
Akasin abin da mutane da yawa za su yi tunani, Jessica ta bayyana cewa gidan su suna rayuwa cikin salama da zaman lafiya. Ta ce: “Muna son zaman lafiya, ina son mijina sosai. “Ban taba kishin ganin ya shigo da mata da yawa ba. Mutum ne mai adalci .Duk abin da yake yi koyaushe daidai ne ba kuskure baya aikata abu sai ya yi tunani.”
A kan yadda David ke yake ciyar da iyalin sa,Afrimax ta ruwaito cewa ya kasance mai bada tarihi kuma yana samun kuɗi da wannan sana’ar.

Martanin masu amfani da kafafen sada zumunta

Elizabeth Otieno Nyaure ta ce:
Na fito daga dangin da ake auren mace fiye da daya kuma yana da kyau a cikin iyali. Mata da yara suna shan wahala kuma dangi suna cin riba mai yawa.”

Immaculate Nyongesa ya ce: “Ya na mutuwa za a bar marayu sama da 200 da zawarawa 50, hikimarsa ta taba ba shi shawarar makomar yaran nan, Solomon ya kasance mai arziki a gaskiya fiye da tunani,ina tausayin matan nan da suka makance akan shi”.

Tazalike Lydia ta ce: “A gaskiya mutumin nan yana da gaskiya fiye da sauran mazan da suke daukar mata su kai gida,maza da yawa suna can suna daukar mata a gidajen kwana.”

Yar shekara 22 ta fada tarkon soyayyar tsoho mai shekaru 88, har ya dirka mata ciki

Chibalonza mai shekaru 22 ta fada soyayya da tsohon da yaci ace ya yi jika da ita, Kasher Alphonse, mai shekaru 88 a duniya, Legit.ng ta ruwaito.

Mutumin ya sanar da Afrimax English cewa duk da bambancin shekaru 66 da ke tsakaninsu, su na matukar kaunar juna kuma sun fahimci juna kwarai.

Matarsa ta farko ta rasu
Matar Alphonse ta farko ta rasu ne shekaru 2 da su ka gabata. Kuma yanzu haka shekarunsu 2 tare da Chibalonza cike da soyayya da kauna.

Alphonse ya auri matarsa ta farko a shekarar 1954 wacce ta haifa masa yara bakwai bayan shekaru 24. Daga nan ne ta kwanta dama.
Ya bayyana yadda ya dinga fama yana ayyukansa da kansa ba tare da wani ya taimaka masa ba kafin ya hadu da Chibalonza.

Ba su riga sun yi aure ba
Ya gamu da Chibalonza ne lokacin tana da shekaru 20 kuma ta bayyana cewa a shirye take da ta zauna da shi a matsayin matarsa.

“Ba mu riga mun yi aure ba amma kowa ya san soyayyarmu. Na kai wa danginta giya kiret daya da kuma akuya,” a cewarsa.

Ya bayyana cewa bai san yadda yaransa za su dinga yi mata ba idan ya mutu. Ya yi danasani akan cewa ba ya da kudin siya mata fuloti don matarsa ta samu gidan zama.
Chibalonza ta kusa haihuwa
Ya ce da zarar ta haihu za su shirya aure na musamman wanda za a yi shagulgula. Amma dai mutane su na ta ganin rashin dacewarsu sakamakon bambancin shekarun.

Ya ce dansa na farko shekarunsa 66, autansa kuma shekarunsa 50. Ya bayyana yadda ya fuskanci kulubalen rashi cikin ‘yan shekarun nan kasancewar ‘yan fashi sun kai masa farmaki a shago.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe