23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

‘Yar shekara 22 ta fada tarkon soyayyar tsoho mai shekaru 88, har ya dirka mata ciki

Labarai‘Yar shekara 22 ta fada tarkon soyayyar tsoho mai shekaru 88, har ya dirka mata ciki
  • Duk da bambancin shekaru 66 da ke tsakanin Chibalonza da Kasher Alphonse, amma hakan bai dakatar da su daga fara soyayya ba
  • Yanzu haka, ‘yar shekara 22 ta fada soyayya da tsoho mai shekaru 88, kuma batun da ake yi har ya dirka mata ciki za su haifi dansu na fari
  • Sai dai Alphonse ya shiga damuwa kasancewar yaransa da su ka girmeta za su iya cutar da ita da zarar sun ga ba ya da rai

Chibalonza mai shekaru 22 ta fada soyayya da tsohon da yaci ace ya yi jika da ita, Kasher Alphonse, mai shekaru 88 a duniya, Legit.ng ta ruwaito.

Mutumin ya sanar da Afrimax English cewa duk da bambancin shekaru 66 da ke tsakaninsu, su na matukar kaunar juna kuma sun fahimci juna kwarai.

Matarsa ta farko ta rasu

Matar Alphonse ta farko ta rasu ne shekaru 2 da su ka gabata. Kuma yanzu haka shekarunsu 2 tare da Chibalonza cike da soyayya da kauna.

Alphonse ya auri matarsa ta farko a shekarar 1954 wacce ta haifa masa yara bakwai bayan shekaru 24. Daga nan ne ta kwanta dama.

Ya bayyana yadda ya dinga fama yana ayyukansa da kansa ba tare da wani ya taimaka masa ba kafin ya hadu da Chibalonza.

Ba su riga sun yi aure ba

Ya gamu da Chibalonza ne lokacin tana da shekaru 20 kuma ta bayyana cewa a shirye take da ta zauna da shi a matsayin matarsa.

“Ba mu riga mun yi aure ba amma kowa ya san soyayyarmu. Na kai wa danginta giya kiret daya da kuma akuya,” a cewarsa.

Ya bayyana cewa bai san yadda yaransa za su dinga yi mata ba idan ya mutu. Ya yi danasani akan cewa ba ya da kudin siya mata fuloti don matarsa ta samu gidan zama.

Chibalonza ta kusa haihuwa

Ya ce da zarar ta haihu za su shirya aure na musamman wanda za a yi shagulgula. Amma dai mutane su na ta ganin rashin dacewarsu sakamakon bambancin shekarun.

Ya ce dansa na farko shekarunsa 66, autansa kuma shekarunsa 50. Ya bayyana yadda ya fuskanci kulubalen rashi cikin ‘yan shekarun nan kasancewar ‘yan fashi sun kai masa farmaki a shago.

Miji ya dirkawa surukar shi cikin shege, ya kuma yi alkawarin auren ta a matsayin mata ta 2

A cewar matar, mijin nata ya yi kwanci kwanci ya dirkawa mahaifiyarta ciki bayan ya aikata wanan abun kunyan hakan bai ishe shi ba har yana shirin auren ta a matsayin mata ta biyu.

Da take bada labari ga wakiliyar jaridar Information Nigeria, matar ta nemi da a sakaya sunanta, ta bayyana cewa ta kadu matuka bayan da ta gano cewa mahaifiyarta na dauke da cikin mijinta.

Ga dai labarin matar kamar haka

“A shekarar 2009 mukayi aure ni da kyakkyawan mijina. Muna zaune lafiya, cikin kauna da farin ciki amma kash, na gaza samun ciki da wuri.

“Shekara guda bayan aure na, ban taba batan wata ba, ko bari ban taba yi ba, hakan bai yi wa mijina Ken dadi ba.

“Ya san cewa hakan ba laifina ba ne kuma shi ma matsalar ba daga gare shi take ba saboda mun taba ziyartan wani likita inda ya tabbatar mana da cewa lafiyar mu kalau babu wata matsala.

“A Shekarar 2011, nan ma babu alamar ciki, wanda hakan ya kara haddasa wa mijina damuwa. Mun ziyarci asibitoci ba adadi, masu magungunan gargajiya, Fastoci, duk babu inda bamu je ba amma ba a dace ba.

“Har hakan ta kai ga mijina ba ya iya barci da daddare. Ko yaushe kansa a sama yana lissafin yadda zai bullowa wannan lamari.

“Mahaifiyarsa ta fi kowa daga hankali akan wanan lamari. Har ta kai ga taba Ken shawaran ya kara aure. Ta ke ce masa: “Matarka juya ce bata haihuwa, ka auro wata matar da za ta haifo min jikoki”.

“Duk sanda ta fadi haka ran Kem yana tunzura, saboda yana so na sosai kuma ba zai so yai min kishiya ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe