Wani tsoho da ya shafe shekara 67 a gidan yarin Philadelphia, bayan an yanke masa hukuncin daurin rai da rai, ya nuna turjiya ta kin fita daga gidan yarin, bayan an sallame shi an yi masa afuwa.
Dalilin zuwan tsohon gidan yari
Tsohon mai suna Joseph Ligon, an daure shi ne tun yana ɗan shekara goma sha biyar, a sakamakon zargin kisan wadansu mutane biyu. Tun daga wancan lokaci Ligon ya rasa yancin sa na walwala.

A ranar 20 ga Fabarairun shekara ta 1953, a wajen wata liyafa, Ligon din da abokansa hudu suka yi wa mutane takwas fashi, inda suka kashe biyu daga cikin su har lahira.
Duk tsawon wannan lokaci , Ligon bai tura takaddar neman afuwa ba, wacce ita zata sa a sake shi daga gidan yarin, tare da sanya ido akan sa domin tabbatarda ganin bai sake shiga cikin wata matsala ba.
Baiyi tsammanin za’a iya yi masa afuwa ba
A cewar lauyansa, bai mika takardar neman afuwan ba ne saboda bai yi tunanin ya cancanci a sake shi ba, inda ya shafe shekaru 67 a gidan yari.

Har’ila yau, ya sake samun wata dama a shekarar 2016, amma sai ya gaza yin amfani da ita, saboda tunanin da yake dashi a baya na cewa bazai iya samun sassauci ba.
Idan aka sallami Joseph Ligon, zai tafi ya gudanar da rayuwar sa ba tare da sanya idon hukuma akan sa ba. Amma ya ki karbar afuwar da aka yi masa, bayan abokan zaman sa fursunoni sun amshi tasu afuwar da hannu biyu.
yana jin kurkuku tamkar gida a gareshi
Kasantuwar ya dade a gidan yarin, wadansu ma na ganin cewa bazai iya rayuwa a wani wuri ba kurkuku ba.
Bayan dirkawa mata 2 ciki, an mayar da wanda ya sauya jinsi zuwa gidan yarin maza
Demi Minor mai shekaru 27 ya koma bangaren gidan gyaran halin Garden State Youth daga Edna Mahan a watan Yuni. An daure ta ne bayan tayi yunkurin rataye kanta yayin da ta koma GSCF, Daily Mail ta ruwaito.
A wata wallafa, ta bayyana cewa ma’aikatan gidan gyaran halin sun sa mata ido yayin da aka umarce ta tube don wata mace ta duba ta.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com