28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

RAHAMA SADAU: Shekaru 15 da suka wuce a wannan rijiyar nake dibo ruwa

LabaraiRAHAMA SADAU: Shekaru 15 da suka wuce a wannan rijiyar nake dibo ruwa

Jaruma Rahama Sadau ta wallafa wadansu hotuna, inda ta nunawa masoyanta da mabiyan ta wata rijiya, wacce a cewar ta; a cikin rijiyar ta ke diban ruwa, shekaru goma sha biyar da suka gabata. 

Rahama sadau ta duki hotuna a kauyen da rijiyar take

A cikin yanayi na nishadi, jaruma Rahamar ta dauki hotunan a kauyen dake jihar Gombe wanda tace anan ne ta taso, kuma anan tayi  kuruciya. 

Babban abin da ya baiwa wasu daga cikin mabiyan ta mamaki, shine yadda jaruma Rahamar ta dauki hotunan a garin kuma har ta yada su, tana mai ikirarin cewa ta dibi ruwa a wannan rijiyar shekara goma sha biyar baya. 

Jarumai irinta suna jin kunyar bayyana bayan su

Ba kasafai aka fiya ganin manyan taurari suna nuna wani abu da suka yi a baya ba, musamman idan na wahala ne, saboda yanzu sun sami daukaka, kuma idan suka  bayyana bayan su, kamar za’a yi musu dariya ne, ko kuma suna ganin yanzu sun girmi wancan yanayin na baya. 

Dalilin haka wadansu sukan nuna dama su daga babban matsayi suka taso, koda kuwa sun sha wahala a baya. Amma ita Rahamar hakan ko a jikin ta.

Daga gida ake fara samun tarbiyya, Inji Rahama Sadau

Sau da yawa akan ce wasu jaruman Kannywood suna yin wasu abubuwan da gayya don a dinga cece-kuce akansu wanda wasu ke ganin hakan ne kasuwancinsu.

Wasu na ganin idan har ba a maganar jaruman, kasuwarsu ta mutu. Hakan ke sa wani lokacin da kura ta lafa sai su kara taya da sabuwa bayan wani dan lokaci, Tsakar Gida ta ruwaito..

Musamman masu bibiyar shafin Rahama Sadau na TikTok a ‘yan kwanakin nan za su ga yadda take wallafa hotunanta da shiga da ba ta dace ba.

Wani lokacin ta na wallafa hotunanta tare da maza yayin da ta dafa su ko kuma a yanayin da bai dace ba. Idan mutum bai kula da cewa Rahama ba ce zai iya musanta cewa ita musulma ce ko kuma bahaushiya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe