24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Bayan shekaru 15 yana biyan kudin haya, miji ya fadi warwas bayan gano matarsa ce mai gidan

LabaraiBayan shekaru 15 yana biyan kudin haya, miji ya fadi warwas bayan gano matarsa ce mai gidan

Wani mutum dan kasar Zambia mai suna Martin Stampa ya fadi kasa warwas inda ya sume bayan gane cewa ashe matarsa ce mai gidan hayar da su ke ciki, LIB ta ruwaito.

Manema labarai sun gano cewa ya kwashe shekaru 15 yana biyan kudin hayar kwacha 3500 duk wata. Sannan an gano cewa matar ce ke amsar kudin da sunan za ta kai wa min gidan.

Sai dai an gano cewa matar mai suna Lushomo ta yi hakan ne don ta hukunta mijin wanda ta fahimci cewa yana bin matan bariki.

An samu rahoto akan yadda Martin ya fada wa matarsa cewa ya samu wata budurwa a wajen aurensu kasancewar yana son mace mai tsananin kaifin kwakwalwa don su dinga tattaunawa da hira ta basira.

Wannan lamarin ya hassala Lushomo inda ta fallasa masa sirrin da ta dade tana boyewa. Ta sanar da shi cewa ba ya da kaifin kwakwalwa tunda ya kasa fahimtar cewa ita yake biya kudin haya duk wata don gidan da su ke ciki nata ne.

Bayan jin wannan ne Martins ya rikice ya fadi kasa warwas. Sai da mutane su ka samo ruwa su ka dinga watsa masa don ya falka.

Farashin Naira yana ƙara sauka warwas, ana canzarwa N417.51 ita ce daidai da dala 1

Naira ta ci gaba da faɗuwa yayin da ake siyar da dala kan N417.51 ​​a kasuwar gwamnati a ranar Alhamis.

Hakan na ƙunshe ne a cikin bayanan da aka samu daga shafin yanar gizo na babban bankin Najeriya, wanda ke nuna sakamakon canjin da kuma matsakaicinsa, a ranar Alhamis.

Bayanai sun nuna cewa an sayar da dala kan N417.51 ​​yayin da aka siyo ta kan N416.51.

Da wannan ci gaban, Naira ta samu raguwar darajar a kan dalar Amurka, sa’o’i ashirin da hudu bayan ta samu ‘yar riba a bangaren kasuwar tsaye.

Sai dai shafin yanar gizon FMDQ da ake yin cinikin forex a hukumance, a cikin bayanansa, ya nuna cewa an rufe kudin gida a kan N416.67 zuwa dala ɗaya a kasuwar ranar Alhamis.

Wannan dai ya nuna faduwar darajar kashin 0.3 ko 0.10 bisa dari daga N416.37 da ta yi musanya a mako da ya gabata a ranar Laraba, inda aka samu dala miliyan 109.75 a matsayin musayar kudin ƙasashen waje a ƙarshen kasuwancin ranar Alhamis.

A tsakar rana, Naira ta karkata zuwa N410.00 da kuma kasa da N444.00, kafin rufewa a kan N416.67 a ranar Alhamis, kuma ta tsaya a kan layin da take kasuwanci tun bayan bude kasuwanci a wannan makon.

Dabarun canjin Najeriya na hana masu zuba jari, yana kara hauhawar farashin kayayyaki.
A ranar Talata ne dai karo na karshe da aka rufe kudin a kan Naira 416.67 zuwa dala ɗaya, wanda ya zuwa yanzu, farashin Naira mafi karanci a kasuwannin gwamnati a wannan watan.

A halin da ake ciki, mafi girman farashin da yankin ya yi musanya da kudin Amurka a wannan watan shi ne N415.36 a kan kowanne dala 1 a kasuwar tabo, kamar yadda bayanai na CBN suka nuna a shafin sa na yanar gizo.

Hakan na nufin kawo yanzu kudin ya kara karfi da kashi 4.4 bisa dari bayan da aka samu koma baya a watan Disambar bara lokacin da Naira ta rufe kan N435.00.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe