34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Sojoji zasu iya fata-fata da maboyar ‘yan bindiga cikin minti 15 amma hakan bazai yi amfani ba, matsalar siyasa ce ba ta karfin makamai ba – Inji Ahmad Gumi

LabaraiSojoji zasu iya fata-fata da maboyar 'yan bindiga cikin minti 15 amma hakan bazai yi amfani ba, matsalar siyasa ce ba ta karfin makamai ba - Inji Ahmad Gumi

A wata hirar hadakar ‘yan jarida da cibiyar bincike da rahoton kwakwaf (ICIR) ta gabatar tare da shehin malamin nan Ahmad Gumi, malamin ya fadi hanyoyin da za’a kawo karshen matsalar ‘yan bindiga, wadda ta tagayyara wasu bangarori na Arewa maso yammacin Najeriya. 

Sojoji zasu iya fatattakar yan bindiga cikin minti 15

Shehun malamin yace, soji suna da karfi sosai, za su ma iya tasar gari guda a cikin minti goma sha biyar 15.

yan bindiga
Sojoji zasu iya fata-fata da maboyar ‘yan bindiga cikin minti 15 amma hakan bazai yi amfani ba, matsalar siyasa ce ba ta karfin makamai ba

“Sojin Najeriya suna da makamai masu karfi da zasu iya wargaje dukkanin maboyar yan bindiga, haka zalika Sojin sama, suna da dukkanin kayan aikin da zasu iya yin faca-faca da Kaduna, idan aka basu izini, amma hakan bazai yi aiki ba, duk da suna da wadannan kayan aikin, na kawar da yan bindiga “. 

Gumin ya kara da cewa, ‘yan bindigar nan sun ware i’nasu sun koma daji, saboda haka sanya jami’an tsaro su gama da su, bazai yi aiki ba. Mun rasa makama, wajen yakar yan bindiga, sakamakon haka matsalar sai kara fadi take yi. 

Matsalar ta siyasa ce ba ta karfin makamai ba

A cewar Gumin, matsalar ta siyasa ce. Inda ya kara da cewa lokacin da ya je gurin yan fashin dajin, sun yi tsammani yaje tare da wani jami’in gwamnati a matsayin wakilin ta, domin  a yi sulhu, da suka duba suka ga babu jami’in gwamnati ko daya, sai suka koma suka ci gaba da abin da suke yi.

Bello Turji ya saki duk wadanda yayi garkuwa da su kuma ya tuba -Sheikh Gumi

Sananen malamin nan na Najeriya, Sheik Gumi, ya fitar da bayanai akan kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, na jihar Zamfara, Bello Turji.

Sheikh Gumi ya bayyana dalilin yin kiran sa ga gwamnati

A wata hira da aka yi da malamin a kafar talabijin ta Arise News, Sheikh Gumi ya bayyana dalilin sa na yin kira ga gwamnatin tarayya da kafa ma’aikatar harkokin da su ka shafi barayin daji da makiyaya.

Sheikh Gumi yace:

Gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen sake canja su “. Ba wai ina kira ne cewa a yi musu wani abu na musamman ba, saboda wadannan mutanen an dankwafe su. Babu wanda ya taɓa cewa an dankwafe su. Ina makarantun su, asibitocin su, titunan su, da kuma ruwan shan su suke? Babu abin da suke samu daga kason ƙasa. Wannan tsari ne da aka daɗe ana tafiya akan sa. Wanne tabbaci nake da shi?

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe