24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Bidiyon Malam Ali na Kwana Casa’in yana kutuntuma wa Rayya ashar a wurin daukar fim

LabaraiKannywoodBidiyon Malam Ali na Kwana Casa'in yana kutuntuma wa Rayya ashar a wurin daukar fim

Wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani ya bayyana Sahir Abdul, wanda aka fi sani da Malam Ali a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango yana kutuntuma wa Rayya, abokiyar sana’arsa ashar na cin mutunci, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Alamu na nuna cewa a wurin daukar fim din aka yi wannan rikicin don daga bidiyon za ka gane cewa a gidan Bawa Mai Kada aka dauki bidiyonsa yana zagin.

A cikin bidiyon an ji inda Malam Alin yake korafi yana cewa ya zo wurin daukar fim ba shi da lafiya amma babu wani cikinsu da ya tambaye shi ya jikinshi kuma ana cewa an kula da shi.

An ji yana auna zagi sosai har yake cewa idan an ga dama a cire shi daga aikin.

Bayan wannan bidiyon, an ji inda Malam Alin ya kara tura wa Rayya zagi kwando-kwando yana kiranta da jahila inda itama ta mayar masa da martani da zage-zage masu zafi ta WhatsApp.

Kawo yanzu dai babu wanda yasan dalilin yiwa juna wadannan zage-zagen.

Kuci gaba da bibiyarmu don gano asalin abinda ya hada su rikicin.

Allah yasa mu dace, Ameen.

Hadiza Gabon ta sa an kama jarumi Auwal Isa West kan ashariyar da ya dinga kunduma mata a wani bidiyo

A jiya Litinin ne 11 ga watan Oktoba, muke samun labari daga shafin Instagram na Mufeeda Rasheed kan hatsaniyar da ke tsakanin Auwal Isa West da Hadiza gabon, inda ta bayyana tuni jarumar tasa an kama jarumin da ya yi mata zagin cin mutunci.ashar

Kamar yadda muka ruwaito a baya, Hadiza ta yi wasu rubuce-rubuce da maganganu kan jaruman Kannywood da cewar sun yi shishshigi wajen shigewa jarumin da ya lashe gasar Big Brother Naija, wato White Money, inda suka je suna hotuna da shi, a cewar ta da nasu ne baza su yi musu haka ba.

Hadiza Gabon ta kara da cewa jaruman na Big Brother ko damuwa ba su yi ba don su wallafa hotunansu a shafukansu na sadarwa, balle ma su yi musu Re-post.

Sai dai wannan magana wasu sun dauke ta a matsayin rashin kunya ganin cewa akwain manyan jiga-jigan Kannywood cikin wadanda suka halacci taron da aka shirya, irin su Ali Nuhu, Baba Karami, Adam A Zango, Abba Elmustapha da sauran su.

Hakan ya sanya furodusa Alhaji Sheshe da Auwal Isa West suka yiwa jarumar raddi, sai dai kuma shi Auwal West a nasa raddin ya kama sunan Hadiza Gabon ya kuma rufe raddin nasa da zagi na rashin mutunci.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe