27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

2023:Karon farko Atiku da Wike za su sulhunta

Labarai2023:Karon farko Atiku da Wike za su sulhunta
Untitled 1 1140x570 1

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, sun amince da kawo karshen sabanin dake tsakaninsu.

Sun cimma matsaya

Sun cimma wannan matsaya ne a ranar Alhamis a wani taro da suka yi a Abuja a gidan tsohon ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Jerry Gana.
Wannan dai shi ne karon farko da shugabannin biyu za su gana tun bayan da Atiku ya yi watsi da Mista Wike ya nada gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairun 2023.

Yana cikin jerin sunayen da aka bada na mataimakin shugaban kasa

Nadin dai ya harzuka Mista Wike, wanda ya kasance kan gaba a cikin sunaye uku da kwamitin ba da shawarar tantance wanda zai tsaya takarar mataimakin shugaban kasa su ka bayar.
Lamarin dai ya haifar da rikici a jam’iyyar, inda suma masu ruwa da tsaki na korafin yadda shugabancin jam’iyyar ke yi wa Arewa katutu.

An bukaci shugaban jam’iyya ya yi murabus

A wani taron da aka shirya a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja, Mista Wike da sauran ‘yan jam’iyyar sun bukaci shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu da ya yi murabus, wanda hakan ya kasance wani bangare na sharudan sulhu da Atiku.
Sai dai a wani taro da aka yi a ranar Talata, kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa sun kada kuri’ar amincewa da Mista Ayu yayin da kwamitin amintattu su kuma suka kafa kwamitin da zai gana da Mista Wike da sauran mutanen sa.
Sai dai kuma a ranar Juma’a a taron da Mista Gana ya jagoranta, shugabannin biyu sun amince da kafa wani kwamiti cikin sa’o’i 48 da zai tsara tsarin sasantawa a tsakaninsu.
Atiku da Mista Wike sun amince da nada mutane bakwai kowannen su daga cikin kwamitin, akan wanda zai duba dukkan batutuwan da kungiyar ta Mista Wike ta gabatar tare da baiwa shugabannin biyu shawara kan yadda za a magance su.
Sai dai Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa ba ta tabbatar da ko shugabannin biyu ne suka kafa kwamitin da mambobi ba.Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, bai amsa kiran wayarsa da safiyar Lahadi ba kan wannan rahotan.

2023: Atiku Abubakar yayi muhimman naɗe-naɗe a tawagar yaƙin neman zaɓen sa

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya naɗa kakakin yaƙin neman zaɓen sa na neman takarar shugabancin ƙasar nan.

An bayyana sunayen mutanen da ya naɗa
Atiku Abubakar ya naɗa Dino Melaye da Daniel Bwala a matsayin kakakin yaƙin neman zaɓen sa. Jaridar The Punch ta rahoto.

Mai taimaka wa Atiku kan harkokin sadarwa, Paul Ibe, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Alhamis.

Ibe yace nan take naɗin ya fara aiki.

Asalin mutanen da ya naɗa kakakin yaƙin neman zaɓen sa
Dino Malaye, tsohon sanata a majalisar dattawa ta 8, haifaffen jihar Kogi ne. Ya wakilci Kogi ta Yamma a majalisar dattawa.

Daniel Bwala, wanda kafin zuwa yanzu, babban ƙusa ne a jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC), lauya ne kuma haifaffen jihar Adamawa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe