34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Dan uwan Buhari ya fice daga APC, ya gana da Atiku

LabaraiDan uwan Buhari ya fice daga APC, ya gana da Atiku
FB IMG 16599130759565121

Mamba mai wakiltar mazabar Daura/Sandamu/Maiadua, Fatuhu Muhammad, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki bayan ganawarsa da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

Ya sha kaye a zaben fidda gawain

Mista Muhammad, wanda ya kasance Da ne ga shugaba Muhammadu Buhari, a ranar 28 ga watan Mayu, ya sha kaye a zaben fidda gwani da akayi na yan majalisa a jam’iyyar APC.
A wata wasika da dan majalisar ya aikewa shugaban jam’iyyar APC na unguwar Sarkin Yara ‘A’ da ke Daura, ya godewa jam’iyyar APC da ta ba shi damar yi wa al’ummarsa hidima.
“Ina so in sanar da ku cewa na yi murabus daga jam’iyyar All Progressives
Congress (APC) wanda zai fara aiki nan take daga ranar Laraba 13 ga wata
Yuli, 2022. A haɗe a nan akwai takardar Rijista na,na Jam’iyyar tare da lamba ta
KT/DRA/10/00002.
“sannan ina mika godiya ta ga Jam’iyyar saboda damar da aka ba ni na yi wa al’ummar
Daura/ Sandamu/ Mai ‘Adua Federal Constituency hidima a lokacin da nake aiki da
jam’iyyar,ina ma kowa fatan alkairi
” dan majalisar ya rubuta.

Ya gana da Atiku

DAILY NIGERIAN  ta tattaro cewa dan majalisar ya kai kara a hedikwatar jam’iyyar ta kasa kan zargin haramtawa wanda ya lashe zaben fidda gwani da kuma wasu kura-kurai da suka gudana a lokacin zaben, amma jam’iyyar ta yi biris da hakan.
Majiya mai tushe ta bayyana cewa Mista Muhammad ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a ranar 21 ga watan Yuli a Abuja inda ya kammala shirin shiga jam’iyyar ta PDP tare da taya Atiku Abubakar yakin neman zabe.

Har yanzu ni ɗan a mutun Buhari ne -Ɗaya daga cikin fasinjojin da aka sako

Ɗaya cikin mutanen da aka sako waɗanda aka sace a harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna, Hassan Usman, ya bayyana cewa har yanzu shi ɗan a mutun shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne.

Kafin a sako shi a ranar 25 ga watan Yuli, Usman wanda lauya ne tare da matarsa Amina, suna daga cikin fasinjojin da aka sace a harin a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Usman, wanda ya kwashe sama da kwanaki 100 a tsare, yana daga cikin mutanen da aka gani ƴan ta’adda na duka a cikin wani bidiyo.

Ya yarda cewa gwamnatin Buhari ta gaza a fankin tsaro
Jaridar The Punch ta rahoto cewa da yake hira da ICIR, Usman ya amsa cewa duk da har yanzu shi masoyin Buhari ne, gwamnatin sa ta gaza a fannin tsaro.
Har yanzu ni masoyin Buhari ne amma a fannin tsaro, zan iya cewa gwamnatin sa bata taka rawar gani ba.

Domin ɗaya daga cikin manyan alhakin dake kan su shine ganin cewa lafiya da dukiyar al’umma an tabbatar da tsare su a gwamnati.

Amma a yadda lamura suke yanzu, zan iya cewa wannan gwamnatin ta gaza sosai a wannan fannin. Duk da maƙudan kuɗaɗen da ake warewa fannin tsaro a Najeriya, har yanzu babu wani abin a zo a gani.

Ya bayyana halin da suka tsinci kan su ciki a hannun ƴan ta’adda
Da yake magana dangane da halin da suka shiga a hannun ƴan ta’addan, sai ya kada baki yace:

Gaskiya mun sha baƙar azaba. Tun lokacin da aka kama mu, sai da muka yi doguwar tafiya ta kimanin kwana uku kafin muka isa wani sansani inda aka tsare mu na kusan watanni huɗu.
Saboda tun lokacin da muka isa wannan sansanin, kusan mun dinga yin barci a ƙasa ne, duk rana, ruwa muna nan a wurin. Sauro da macizai sun dinga cizon mu na tsawon lokaci.

Mun kashe fiye da macizai 10 sannan da wasu dabbobin kamar kunamu da sauran su.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe