31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan banga biyu, sun yi awon gaba da wasu amarya da ango a garin Katsina

Labarai‘Yan bindiga sun kashe ‘yan banga biyu, sun yi awon gaba da wasu amarya da ango a garin Katsina
Yusuf Bishir and wife. abducted 666x570 1

Wasu ‘yan bindiga sun kashe’yan banga guda biyu tare da yin garkuwa da wasu mazauna unguwar Shola Quarters a cikin birnin Katsina da safiyar Lahadi.
Wadanda aka yi garkuwa da su a harin da ya dauki same day sa’o’i sun hada da wasu ango da amarya.
Shola Quarters anguwace da ke bayan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (Tsohon Federal Medical Center) Katsina.
Yankin wanda ya kasance a tsakiyar birnin na katsina wanda ke dauke da shaguna,gidaje har ma da ofisoshin gwamnati.

Yan ta’adda sun manage yankin

PREMIUM TIMES ta tattaro daga mazauna yankin da suka nemi a sakaya sunansu cewa ‘yan ta’addan sun mamaye yankin ne da misalin karfe 1:25 na safe inda suka shafe sama da awa daya suna gudanar da ayyukansu ba tare da isowar jami’an tsaron jihar ba.
“’Yan banga ne akwai sukayi kokarin tunkarar yan bindiga Inda ‘yan bindigan suka kashe biyu daga cikin ‘yan bangan tare da raunata wasu ‘yan banga su biyu. ‘Yan banga sun koma gidajensu a lokacin da ‘yan fashin suka ci karfinsu, sai yanzu da safe ne muka fito muka daukin gawarwakin mutum biyu tare da dauke wadanda suka jikkata zuwa asibiti,” inji mazaunin garin.

An yi garkuwa da amarya da ango

Usman Masanawa, wani kani ga ango da amaryan da aka sace, ya bayyana yadda aka yi garkuwa da su.
Wadannan hare-haren sun zama abin ban tsoro.Na kasance ina zama a yankin amma ba ni da wani zaɓi illa in chanza matsuguni, Da suka zo sai Yusuf Bishir (mijin) ya kira ni ya sanar da ni amma ba abin da zan iya yi. Mun je can a safiyar yau kuma ba ta kofar shiga gidan suka shiga ba; sun farfasa katangar ne suka shiga gidan,” in ji Malam Masanawa.
“Muna bukatar lokaci don sanin wadanda aka sace da wadanda suka tsorata suka gudu zuwa wasu yankuna,” in ji shi.

Yan banga sun Sami raimi

Ya kara da cewa baya ga ‘yan banga da suka samu raunuka, an kai sauran mazauna garin da suka samu raunukan harbin bindiga zuwa asibitin koyarwa domin yi musu magani.
Da Jaridar PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar kan harin,Gambo Isa, ya mayar da martani ta WhatsApp.

“Jami’an mu suna kan aiki kuma za su yi bayani dalla-dalla a kan aikin.”

Ya ki bada karin bayani.

Ƴan sanda sun cafke riƙaƙƙen ɓarawo mai yaudarar mata zuwa otal yana musu sata

Jami’an ƴan sanda na Surulure a jihar Legas sun cafke wani ɓarawo mai suna Ifeanyi Odieze Ezenagu mai shakaru 34 bisa zargin tafka laifin sata ga mata daban-daban, inda yake kwace musu ɗan abin hannun su.

Ya sacewa mata da dama abun hannun su
Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa a wata sanarwa da kakakin hukumar ƴan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya fitar, yace wanda ake zargin ya sacewa matan wayoyin hannu ƙirar iPhone 12 guda uku, iPhone 11 Pro Max guda biyu, iPhone XR guda ɗaya, wayar Nokia guda ɗaya, agogon hannu guda ɗaya sannan da sarƙar zinare guda ɗaya.

Waɗanda kimanin darajar kuɗin su ya kai N2,368,000, bayan ya yaudare su zuwa otal, inda yake sanya musu abin maye a abin sha, wanda yake sanya su barci mai nauyi.
Binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa wanda ake zargin bai da sanannen wurin zama, amma yana yaudarae mata zuwa otal daban-daban inda yake basu ƙwaya sannan ya sace musu kayayyaki

Binciken ya kuma ƙara bayyana cewa ya yi sata ga sama da mata talatin tun sanda ya fara wannan baƙar sana’ar ta sa.

Yayin da aka samu ƙwace abubuwan da ya sace kafin ya rabu da su, ana cigaba da bincike domin zaƙulo masu siyan kayayyakin satar a hannun sa. Zaa miƙa su gaban kotu bayan kammala bincike.

Hukumar ƴan sanda ba za ta saurara ba wurin daƙile ɓata gari
Hundeyin ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar Legas, CP Abiodun Alabi, ya tabbatar wa da mutanen jihar cewa hukumar su ba za tayi ƙasa a guiwa ba wurin tabbatar da kawar da dukkanin wasu ɓata gari a jihar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe