28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Wani Alhaji daga jihar Kano ya rasu a Saudiyya

LabaraiWani Alhaji daga jihar Kano ya rasu a Saudiyya

Wani Alhaji ɗan jihar Kano, Sani Idris Muhammad ya rasu a Saudiyya a lokacin hajjin bana na wannan shekarar 2022.

Hukumar kula da jindaɗin Alhazai ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar Alhajin a ƙasa mai tsarki. Jaridar The Punch ta rahoto

Babban magatakardan hukumar, Alhaji Muhammad Abba-Danbatta, ya bayyana hakan ga ƴan jarida a ranar Asabar.

An bayyana garin da Alhajin ya fito

Yace Alhaji Idris-Muhammed wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Madobi ta jihar, ya rasu ne a ranar Asabar bayan wata ƴar gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti a birnin Makka.

An birne marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a maƙarbartar Shira ta masallacin Harami a birnin Makka.

Abba-Danbatta yayi adduar Allah ya jiƙan marigayin sannan ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan marigayin.

Adadin Alhazan Najeriya da suka rasu a bana a Saudiyya

Alhaji Idris Muhammad shine mahajjaci na huɗu da ƴa rigamu gidan gaskiya daga Najeriya, a yayin gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2022.

Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi jihar Nasarawa, ta rasu a ranar 29 ga watan Yuni, bayan gajeruwar rashin lafiya inda aka binne ta a Makka, yayin da Hajiya Hasiya Aminu daga Zaria, jihar Kaduna ta rasu a ranar Arfah jim kaɗan bayan ta dawo filin Arfah.

Muma anan Labarunhausa.com muna addua’r Allah ya jiƙan su da rahama ya kuma gafarta musu ya kyautata namu ƙarshen.

Hajjin bana: Wani alhaji malamin addini ya rasu a Saudiyya

A wani labarin da muka kawo muku kuma wani Alhaji malamin addini ya rasu a ƙasa mai tsarki. Malamin addinin ya fito ne daga jihar Gombe dake a yankin Arewa maso Gabas a tarayyar Najeriya.

A yayin da alhazai ke shirin dawowa gida Najeriya, an ƙara samun rasuwar wani alhaji, malami kuma mamba a tawagar malamai ta hukumar jinɗaɗin alhazai ta ƙasa wato NAHCOM.

Malamin addinin, Dr Abdulrahman Maigona daga jihar Gombe ya rasu ne jiya kamar yadda sanarwa daga shugabar watsa labarai ta hukumar jinɗaɗin mahajjata musulmai ta jihar Gombe,  Hajiya Hauwa Mohammad, ta nuna. Jaridar The Punch ta rahoto.

Maigona, ya rasu ne a masaukin sa dake a otal ɗin Namma Muwada bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe