28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Ƴan sanda sun cafke riƙaƙƙen ɓarawo mai yaudarar mata zuwa otal yana musu sata

LabaraiƳan sanda sun cafke riƙaƙƙen ɓarawo mai yaudarar mata zuwa otal yana musu sata

Jami’an ƴan sanda na Surulure a jihar Legas sun cafke wani ɓarawo mai suna  Ifeanyi Odieze Ezenagu mai shakaru 34 bisa zargin tafka laifin sata ga mata daban-daban, inda yake kwace musu ɗan abin hannun su. 

Ya sacewa mata da dama abun hannun su

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa a wata sanarwa da kakakin hukumar ƴan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya fitar, yace wanda ake zargin ya sacewa matan wayoyin hannu ƙirar iPhone 12 guda uku, iPhone 11 Pro Max guda biyu, iPhone XR guda ɗaya, wayar Nokia guda ɗaya, agogon hannu guda ɗaya sannan da sarƙar zinare guda ɗaya.

Waɗanda kimanin darajar kuɗin su ya kai N2,368,000, bayan ya yaudare su zuwa otal, inda yake sanya musu abin maye a abin sha, wanda yake sanya su barci mai nauyi.

Binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa wanda ake zargin bai da sanannen wurin zama, amma yana yaudarae mata zuwa otal daban-daban inda yake basu ƙwaya sannan ya sace musu kayayyaki

Binciken ya kuma ƙara bayyana cewa ya yi sata ga sama da mata talatin tun sanda ya fara wannan baƙar sana’ar ta sa.

Yayin da aka samu ƙwace abubuwan da ya sace kafin ya rabu da su, ana cigaba da bincike domin zaƙulo masu siyan kayayyakin satar a hannun sa. Zaa miƙa su gaban kotu bayan kammala bincike.

Hukumar ƴan sanda ba za ta saurara ba wurin daƙile ɓata gari


Hundeyin ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar Legas, CP Abiodun Alabi, ya tabbatar wa da mutanen jihar cewa hukumar su ba za tayi ƙasa a guiwa ba wurin tabbatar da kawar da dukkanin wasu ɓata gari a jihar.

Ya kuma roƙi yan Najeriya da su jajirce sannan su kawo rahoton duk wani abin da basu yarda da shi ba ga jami’an tsaro.

Ƴan sanda sun kama wani matashin barawo da ya kware wajen satar akwatinan talabijin a otal-otal

A wani labarin na daban kuma ƴan sanda sun cafƙe wani ɓarawo wanda ya ƙware wurin satar talabijin a otal-otal.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Edo, sun damke wani barawo mai suna Ahmed Ibrahim, wanda ya kware wajen satar talabijin ta bango a Otal a jihar. 

An tabbatar da cewa, barawon yana kama daki ne a hotal din, kuma idan ya gama zaman sa sai ya sace talabijin daga dakin ya tafi da ita. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe