Jarumar a masana’antar fina-finai ta Nollywood, Mary Remmy Njoku, ta nuna adawar ta kan masu cewa wurin mata yana a ɗakin girki ne.
Jarumar ta kuma soki mutanen dake da irin wannan tunanin na cewa mata a ɗakin girki aka san su, a wani rubutu da tayi a shafin sada zumunta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Jarumar ta nuna cewa maza sun fi mata sabawa da ɗakin girki amma wanda ake samun kuɗi a ciki
Njoku wacce tayi nuni da cewa sama da kaso 78 na manyan masu dafa abinci na duniya maza ne, ta ƙara da cewa yakamata a fara jinjinawa matan aure domin da ace ana biyan su kuɗin aikace-aikacen da suke yi, da sun fi wasu shugabannin banki samun kuɗaɗe.
Ta kuma ƙara nuni da cewa maganar gaskiya itace maza sun fi mata sabawa da ɗakin girki amma ɗakin girkin da ake biya inda suka kyale mata da ɗakin girkin da ba a biya su kula da shi.
Jarumar ta rubuta a shafin Instagram ɗin ta cewa:
Yakamata mu koyi jinjinawa matan aure nagari. Domin da ace ana biyan su bisa dukkanin aiyukan da suke yi, da sun samu kuɗaɗe fiye da wasu shugabannin banki.
Jarumar na auren shahararren ɗan kasuwa
Mary Njoku na auren shahararren ɗan kasuwa kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa gidan talabijin na iROKO TV, Jason Njoku, sananna ce akan matsayar ta ganin mata sun samu gaskiya, daidaito da mutuntawa.
Za a fara biyan matan aure albashi a kasar Kenya
A wani labarin na daban kuma, matan aure za su fara samun albashi a ƙasar Kenya. Wata kotu ce dai a ƙasar ta zartar da hukuncin saboda la’akari da aikin da matan aure suke yi, ya cancanci su samu albashi.
Wata babbar kotu a kasar Kenya ta yi karin haske akan tsarin fara biyan matan aure albashi, inda ta bayyana zama matar aure a matsayin aikin yi da ya kamata a biya su albashi.
A wani rahoto da jaridar Kenyans.co.ke ta ruwaito, Mai Shari’a Teresiah Matheka, ta bayyana cewa rashin adalci ne kotu su bayyana cewa matan aure basa taimakawa wajen kawo cigaba ta fannin tattalin arziki a cikin iyali.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com