34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Har yanzu ni ɗan a mutun Buhari ne -Ɗaya daga cikin fasinjojin da aka sako

LabaraiHar yanzu ni ɗan a mutun Buhari ne -Ɗaya daga cikin fasinjojin da aka sako

Ɗaya cikin mutanen da aka sako waɗanda aka sace a harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna, Hassan Usman, ya bayyana cewa har yanzu shi ɗan a mutun shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne.

Kafin a sako shi a ranar 25 ga watan Yuli, Usman wanda lauya ne tare da matarsa Amina, suna daga cikin fasinjojin da aka sace a harin a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Usman, wanda ya kwashe sama da kwanaki 100 a tsare, yana daga cikin mutanen da aka gani ƴan ta’adda na duka a cikin wani bidiyo.

Ya yarda cewa gwamnatin Buhari ta gaza a fankin tsaro

Jaridar The Punch ta rahoto cewa da yake hira da ICIR, Usman ya amsa cewa duk da har yanzu shi masoyin Buhari ne, gwamnatin sa ta gaza a fannin tsaro.


Yace:

Har yanzu ni masoyin Buhari ne amma a fannin tsaro, zan iya cewa gwamnatin sa bata taka rawar gani ba.

Domin ɗaya daga cikin manyan alhakin dake kan su shine ganin cewa lafiya da dukiyar al’umma an tabbatar da tsare su a gwamnati.

Amma a yadda lamura suke yanzu, zan iya cewa wannan gwamnatin ta gaza sosai a wannan fannin. Duk da maƙudan kuɗaɗen da ake warewa fannin tsaro a Najeriya, har yanzu babu wani abin a zo a gani.

Ya bayyana halin da suka tsinci kan su ciki a hannun ƴan ta’adda

Da yake magana dangane da halin da suka shiga a hannun ƴan ta’addan, sai ya kada baki yace:

Gaskiya mun sha baƙar azaba. Tun lokacin da aka kama mu, sai da muka yi doguwar tafiya ta kimanin kwana uku kafin muka isa wani sansani inda aka tsare mu na kusan watanni huɗu, sannan zama a wannan wurin abu ne mai ciwo matuƙa.

Saboda tun lokacin da muka isa wannan sansanin, kusan mun dinga yin barci a ƙasa ne, duk rana, ruwa muna nan a wurin. Sauro da macizai sun dinga cizon mu na tsawon lokaci.

Mun kashe fiye da macizai 10 sannan da wasu dabbobin kamar kunamu da sauran su.

Musayar ciniki ne sako fasinjojin jirgin ƙasan Abj-Kd da harin yarin Kuje -Ɗan majalisar APC

Wani ɗan majalisar wakilai ta tarayya (APC Gombe) Abubukar Yunus, yayi zargin cewa harin gidan yarin Kuje da kuma sakin wani rukuni na fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna, ka iya zama bani gishiri in baka manja.

Abubakar Yunus yana magana ne a lokacin wata hira a gidan talabijin na Channels TV a shirin su na ‘Siyasa a yau’ a ranar Talata

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe