31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yadda ƴar Najeriya mai kwalin HND ta samu gurbin karatun digirin digir kyauta har 7 a Amurka

IlimiYadda ƴar Najeriya mai kwalin HND ta samu gurbin karatun digirin digir kyauta har 7 a Amurka

Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Islamiyat Ojelade, mai kwalin HND ta tsallake duk wani ƙalubale akan hanyar ta inda ta samu gurbin karatu kyauta har guda 7 domin yin digirin digir a ƙasar Amurka.

Islamiyat na da kwalin HND, inda ta karanci  Science Laboratory Technology, a kwalejin kimiyya ta tarayya dake Ilaro. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Masu kwalin HND ba kasafai suke samun wannan damar ba

Za a yi tunanin cewa dole sai Islamiyat ta fara yin digirin digirgir (masters) ko sharar fagen sa, kafin samun wannan damar musamman yadda ake bambanta masu digiri da HND a Najeriya.

Amma abin mamakin shine gurbin karatun na kyauta na digirin digir (PhD) ne, kai tsaye daga HND.

Ga abinda budurwar ta rubuta a shafin LinkedIn ɗin ta:

Duba da bambancin dake akwai a tsakanin digiri da HND a Najeriya, naji tsoro sannan na rasa abinyi bayan na kammala karatu na.

Ina mai farin cikin sanar da ku cewa zan fara karatun digirin digir (PhD) ɗina a fannin Chemistry a jami’ar jihar Florida,  Tallahassee, Florida, a Amurka a wannan kakar mai zuwa, bayan na samu guraben karatu kyauta daga jami’o’i 7 a ƙasar Amurka, da kwalin HND ɗina a fannin Science Laboratory Technology (Chemistry).

Sunayen makarantun da ta samu gurbin karatun na kyauta

Makarantun da ta samu gurbin karatun sune, jami’ar jihar Florida, jami’ar Massachusetts Armherst, jami’ar Kansas, jami’ar Kentucky, jami’ar Texas ta Arewa, kwalejin kimiyya ta Rensselaer, da jami’ar Marquette.

Zakaran da Allah ya nufa da chara:Bankin duniya ta nemi yarinyar da ke lissafi kamar kwamfuta

A wani labarin kuma bankin duniya na neman yarinyar dake lissafi kamar kwamfuta. Haziƙar ɗalibar yarinyar ta fito ne daga jihar Kano a Arewacin Najeriya.

Saratu Dan-Azumi, wata ‘yar matashiya daga jiharKano ta sake samun daman gurbin karatu saboda kwakwalwan da Allah ya bata na kwarewa a fannin Lissafi.

Kwanan nan aka gano cewa yarinyar ashe ba ta zuwa makaranta amma duk da haka tana iya lissafin lambobi kamar mai aiki da kwanfuta,wanda har ta yi nssarar samun talafin karatu daga gidauniyar Bashir Ahmad, BAF.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe