27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Wizkid ya gudanar da ƙayataccen wasan casu a Saudiyya, ya kafa wani babban tarihi

LabaraiWizkid ya gudanar da ƙayataccen wasan casu a Saudiyya, ya kafa wani babban tarihi

Shahararren mawaƙin ‘Afrobeats’ ɗan Najeriya, Wizkid ya kafa wani tarihi inda ya zama mawaƙi na farko da ya taɓa jagorar wani babban taron wasanni na duniya.

Taron na wasanni wanda yake gudana yanzu haka anyi shi ne a wurin hutawa na NXT LVL Arena, a birnin Riyadh Boulevard na Saudiyya. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Mawaƙin wanda ya lashe kyautar Grammy ya gudanar da wasa mai ɗaukar hankali a gaban ɗumbin mutane a wurin shagalin Gamers8 eSports, ranar Alhamis 4 ga watan Agusta, 2022.

Wizkid tare da taimakon maƙaɗin sa, Dj Tunez da ƴan tawagar sa, sun nishaɗantar da mutanen da waƙoƙinsa sabbi da tsofaffi.

Wizkid yayi wasa mai ɗaukar hankalin ƴan kallo

Mawaƙin ya gabatar da wasa mai kyau mai ɗaukar hankali da manyan waƙoƙinsa da suka shahara irin su “Essence”, “Ojuelegba”, ‘Joro’, ‘Come Closer’, ‘Beat Of Life’, ‘Mood’, ‘Ginger’, ‘Soco’ da sauran wasu da dama.

Wannan ƙayataccen taron wasannin da yake gudana a Saudiyya, ana kallon sa a matsayin “babban shirin wasanni na esports na duniya”, inda ake yin wasanni da abubuwan nishaɗi da kuma nuna al’adu.

An fara shine a ranar 14 ga watan Yuli sannan an shirya kammala shi a ranar 8 ga watan Satumba, 2022.

Bikin na Gamers8 ya zo da abubuwan ban nishaɗi, ƙayatarwa ga ɗumbin mahalarta wurin.

Zai ƙara yin wani wasan casu a ƙasar Amurka

Wasan Wizkid a wurin dai na zuwa ne makonni kaɗan bayan an bayyana shi a matsayin wanda zai jagoranci bikin Rolling Loud, Miami, na birnin New York.

Wizkid zai gabatar da wasa a wurin tare da sauran shahararrun mawaƙan duniya. Dave zai jagoranci daren farko na buɗe taron a ranar 9 ga watan Satumba, mawaƙin gambara na Amurka, Future zai yi nashi wasan a ranar Asabar 10 ga watan Satumba, yayin da Wizkid zai rufe bikin na kwana uku a ranar 11 ga watan Satumba, 2022.

‘Na rasa abin cewa’ cewar tsohon ɗan wasan da Ahmed Musa ya gwangwaje da maƙudan kuɗaɗe

A wani labarin kuma Ahmed Musa ya gwangwaje tsohon ɗan wasan Najeriya da maƙudan ƙuɗaɗe. Ɗan wasan ya nuna godiyar sa da farin cikin sa bisa samun wannan gagarumar kyautar.

Bassey Etim tsohon ɗan wasan ɗaga ƙarfe na Najeriya ya koma cike ramuka a titi, inda bayyana bidiyon sa na halin da yake ciki yasa Ahmed Musa ya neme shi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe