- Yayin birniya a makabartar Dangamvura, daya daga cikin ‘yan rakon gawar ta nemi wani namiji ya zo su yi lalata akan kabarin
- Take anan wani matashi amsa gayyatar tata sai dai ba a samun kwararon robar da zai yi amfani da shi wurin lalatar da ita ba
- Take anan aka samo shi inda su ka hau lalatar gaban jama’a masu rakon gawar aka dinga ihu ana tunzura su yayin da wasu ke bidiyo
‘Yan sanda a Mutare su na neman masu rakon gawar da su ka yi tsirara kafin fara lalata akan wani kabari da ke makabartar Dangamvura da tsakar rana, Hourlyhits.com ta ruwaito.
Lamarin mai ban mamaki ya auku ne a ranar Alhamis din da ta gabata yayin birniyar wani mai gidan karuwai a Mutare cikin kasar Zimbabwe.
Mummunan al’amarin ya auku ne bayan kammala birne gawar marigayi Maroni Mazvita Karinda.
Tuni jama’a su ka ji labarin wanda aka dinga yadawa a kafafen sada daban-daban bayan ‘yan rakon gawar sun yi bidiyoyi guda biyu.
Tatenda ce ta nemi wani namiji ya zo yayi lalata da ita
Bidiyon ya fara ne bayan wata mata, fitacciyar karuwa wacce aka fi sani da Tatenda ko Mai Keisha, ta fara yin tsirara tana neman wani namiji ya zo yayi lalata da ita.
Hakan ya auku ne gaban duk masu rakon gawar wadanda ba su dade da birne Karinda ba, mai gidan karuwan Sakubva, mai shekaru 45.
Nan da nan wani ya amsa goton gayyatar kuma an fahimci cewa yana yawani zama ne a kusa da titin Sakubva.
Masu rakon gawar sun hada baki su na cewa “bvisa, bvisa, bvisa, bvisa” (ma’ana tube kayanka), inda mutumin ya hau cire kaya.
Sai dai ba a samu kwararon robar yin lalatar ba
Masu kallo sun fara yi musu liki da dalar Amurka yayin da su ka kammala tube kayansu. An dakata daga lalata bayan Tatenda ta nemi yayi amfani da kwararon roba wanda babu shi a lokacin.
Daga bisani an samo shi sannan Tatenda ta ci gaba da harkar da mutumin mutane su na kara zuga su.
Dan uwan mamacin, Fungai ya ce wannan lamarin bai yi wa ‘yan uwansu dadi ba. Sun yi kokarin dakatar da su daga yin aika-aikar amma abin ya ci tura.
Fungai ya ce za a nemo wadanda su ka yi wannan mummunan aikin don hukunta su.
Ana bincike akan wadanda su ka yi aika-aikar
An yi kokarin jin ta bakin Tatenda da mutumin amma abin ya ci tura don ana zargin ta sauya gidan karuwan da ta ke zama. Shi ma mutumin an kasa gano inda yake.
Yayin da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, Sifeta Nobert Muzondo, ya ce za a hukunta wadanda su ka yi mummunan aikin.
“Mun gode muku da ku ka janyo hankalinmu akan lamarin. Kuma za mu tabbatar mun kawo wadanda su ka yi aikin nan har da masu yin bidiyo gaban hukuma don hukunci.
“Ba za mu lamunci irin wannan shashancun ba. Bai dace mutum yayi lalata gaban jama’a ba balle a makabarta yayin fa jama’a ke tunzura shi ba,” inji Sifeta Muzondo.
Kotu ta daure wani matashi bayan karuwa ta mutu su na tsaka da lalata
Wata kotun majistare da ke Akure a Jihar Ondo ta umarci a daure wani Dele Ebenezer, mai shekaru 31 bisa zarginsa da zama sanadiyyar mutuwar wata karuwa, LIB ta ruwaito.
Dan sanda mai gabatar da kara, Omhenimhen Augustine ya sanar da kotu cewa ana zarginsa da halaka Blessing Eze mai shekaru 47, sanadiyyar lalatar da yayi da ita.
Augustine ta bayyana yadda mamaciyar ta shiga mawuyacin yanayi yayin da su ke tsaka da lalatar wacce ta yi sanadin mutuwarta.
Ana zarginsa da aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Yunin 2022, da misalin karfe 4 na safiya a Otal din Cool Corner cikin Ondo, sai dai bai amsa laifin ba.
A cewarsa Augustine, laifin ya ci karo da sashi na 316(2) kuma hukuncinsa na karkashin sashi na 319 na dokar Criminal Code Cap 37. Volume 1, na dokokin Jihar Ondo, 2006.
Lauyan wanda ake zargi, C. O Falana ya bukaci kotu ta ba shi damar yin rantsuwa.
Alkalin kotun, O. R Yakubu ya bukaci a sakaya wanda ake zargin a magarkamar ‘yan sanda sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Yulin 2022.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com