31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Sojoji sun lakada wa dan sanda duka har lahira a Legas

LabaraiSojoji sun lakada wa dan sanda duka har lahira a Legas
Matar aure

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce sojojin da har yanzu ba a tantance ko su waye ba, sun yi wa daya daga cikin jami’inta duka har lahira.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin ta shafin sa na Twitter a ranar Juma’a.
Muna aiki da hukumomin @HQNigerianArmy domin sanin gaskiyar lamarin” ya rubuta.
“Allah ya jikan ka gwarzonmu.

Sojojin sun ja ‘yan sanda zuwa barikin su

Kamar yadda jaridar Daily Independent ta ruwaito, lamarin ya faru ne a ranar Laraba a unguwar Soja ta Ojo da ke Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji sun ja jami’an ‘yan sanda biyu, wadanda ke aiki a matsayin masu kula da sufuri, zuwa barikinsu Daya daga cikin su ya yi nasarar tserewa.

Yan sanda sun tare sojoji

Wata majiya da ta zanta da jaridar ta ce sojojin na tukin mota ne a kan cunkoson kan titi inda jami’an ‘yan sandan suka tare su.
Koda suka ga sun takura musu kawai sojojin su ka hau jami’an ‘yan sandan da dukan tsiya tare da yin garkuwa da biyu daga cikinsu.
Majiyar ta ci gaba da cewa a lokacin da sojojin suka lura cewa daya daga cikin jami’an da suka sace ya sume, sai suka yanke shawarar kai shi asibitin su inda a karshe ya rasu.

An aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mata 3 a Iran bisa halaka mazajen su

Wata amarya mai ƙananan shekaru ƴar ƙasar Iran wacce ta halaka mijin da aka tilasta mata aure tana da shekara 15 a duniya, na daga cikin mata uku waɗanda aka aiwatarwa da hukuncin kisa bisa halaka mazajen su a cikin wannan satin.

Soheila Abadi, mai shekara 25 yanzu, an rataye ta a gidan kurkuru bayan an yanke mata hukunci bisa halaka mijinta akan ‘saɓanin iyali’ a cewar bayanan kotu. Shafin LIB ya rahoto.

An kuma aiwatarwa da wasu mata biyun hukuncin kisa a ranar Laraba bisa laifin halaka mazajen su.

Kotuna ba suyi wa matan da suka halaka mazajen su adalci a ƙasar
Masu rajin kare haƙƙin bil’adama sun yi iƙirarin cewa kusan duk lokacin da mata suka halaka mazajen su, to ana cin zarafin su ne a gida amma kotunan ƙasar Iran basa la’akari da hakan.

Matan guda uku na daga cikin mutane 32 da aka rataye a ƙasar a cikin satin da ya gabata.
Kotuna ba suyi wa matan da suka halaka mazajen su adalci a ƙasar
Masu rajin kare haƙƙin bil’adama sun yi iƙirarin cewa kusan duk lokacin da mata suka halaka mazajen su, to ana cin zarafin su ne a gida amma kotunan ƙasar Iran basa la’akari da hakan.

Matan guda uku na daga cikin mutane 32 da aka rataye a ƙasar a cikin satin da ya gabata.

Ana yawan aiwatar da hukuncin kisa a Iran
Hakan na zuwa a yayin da ake daɗa samun ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar, inda aƙalla mutum 251 aka kashe a farkon watanni 6 na wannan shekarar. A cewar rahoton Amnesty International.

Yawan mutanen ya ninka adadin da aka kashe a shekarar da ta gabata a irin wannan lokacin.

Daga cikin mutum 251 da aka halaka, 146 daga ciki masu laifin kisan kai ne, sannan aƙalla 86 masu laifuffukan ƙwayoyi ne wanda bai cancanci hukuncin kisa ba a dokar ƙasa da ƙasa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe