34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Baba-Ahmed ya bayyana abinda yankin Inyamurai za suyi su samu ƙuri’un ƴan Arewa

LabaraiBaba-Ahmed ya bayyana abinda yankin Inyamurai za suyi su samu ƙuri'un ƴan Arewa

Kakakin ƙungiyar dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, yayi gargaɗi akan kashe ƴan Arewa a yankin Kudu maso Gabas.

Ya shawarci ƴan siyasa masu son ƙuri’un ƴan Arewa

Baba-Ahmed a ranar Juma’a 5 ga watan Agusta, 2022, ya yayi wani rubutu a shafin sa na Twitter inda yake cewa ƴan siyasan da ke son samun ƙuri’un ƴan Arewa a zaɓen 2023, dole su fito su yi Allah wadai da waɗannan kashe-kashen.

Jaridar Pulse.ng ta rahoto cewa kakakin ƙungiyar ta dattawan Arewa, ya koka kan yadda ake ake musgunawa ƴan Arewa a yankin, inda yayi nuni da cewa idan ba a yiwa lamarin tufkar hanci ba, ka iya janyo tsatstsamar alaƙa tsakanin mutane a wasu sassan ƙasar nan.

Ya jaddada cewa dole ne a dai na waɗannan abubuwan da ake yiwa ƴan Arewa.

Dole ne ayi Allah wadai da musgunawa da kashe ƴan Arewa da ake yi musamman a yankin Kudu maso Gabas, sannan dole a daina kashe su.

Dole ne ayi Allah wadai da musgunawa da kashe ƴan Arewa da ake yi musamman a yankin Kudu maso Gabas, sannan dole a daina kashe su.

Abu ne mai matuƙar haɗari saboda yana iya sanya wa dangantaka tayi tsami a tsakanin mutane a wasu sassan ƙasar nan

Muna son mu ji waɗanda ke neman ƙuri’un mu sun yi tir da Allah wadai kan waɗannan ayyukan.

Baba-Ahmed yayi tsokacin kan zaɓen 2023

A kwanakin baya Baba-Ahmed yayi tsokaci kan dalilan da suka sanya zaɓen 2023 ya zama mafi muhimmanci tun shekarar 1999.

Baba-Ahmed yace zaɓen 2023 zai nuna idan ƴan Najeriya sun shirya sauyawa daga tafiyar wargatsewa.

Yayi nuni da cewa zaɓen mai zuwa zai nuna idan Najeriya za ta kama hanyar wargatsewa.

Kwankwaso ya bayyana abinda yankin Inyamurai yakamata su koya daga Tinubu

A wani labarin kuma Kwankwaso ya shawarci yankin Inyamurai kan abinda yakamata su koya daga Tinubu.

Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, ya bayyana zaɓen 2023 a matsayin wata babbar dama ga yankin inyamurai.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala wani taron jam’iyyar a jihar Gombe, Kwankwaso yace yankin inyamurai sun iya kasuwanci kuma mutanen su nada hazaƙa, amma yakamata su koyi siyasa, saboda a ɓangaren siyasa sune koma baya

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe