34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

‘Na rasa abin cewa’ cewar tsohon ɗan wasan da Ahmed Musa ya gwangwaje da maƙudan kuɗaɗe

Labarai'Na rasa abin cewa' cewar tsohon ɗan wasan da Ahmed Musa ya gwangwaje da maƙudan kuɗaɗe

Tsohon ɗan wasan ɗaga ƙarfe na Najeriya, Bassey Etim wanda ake wa laƙabi da ‘Iron bar’ ya godewa Ahmed Musa bisa kyautar da yayi masa ta rabin miliyan.

Wani bidiyo ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda ya nuna tsohon ɗan wasan ɗaga ƙarfen yana cike ramuka a titi a hanyar Ado-Badore a yankin Ajah cikin jihar Legas.

Ahmed Musa ya kira tsohon ɗan wasan

Sportsbrief ta tattaro cewa Musa yayi ido huɗu da bidiyon inda ya nemi da ya haɗu da Bassey Etim. Ɗan wasan na Fatih Karagumruk ya kira shi a kira mai nuna hoton bidiyo.

Ahmed Musa ya tura wa tsohon ɗan wasan maƙudan kuɗaɗe har naira dubu ɗari biyar (N500,000).

Bassey ya nuna godiyar sa inda yake cewa:

Na rasa abin cewa sannan naji daɗi sosai. Wannan muhimmiyar rana ce a gareni bisa amsar irin wannan kyautar. Allah zai albarkace shi da shi da iyalan sa. Nagode sosai sannan naji daɗi.

Yadda labarin halin da Bassey yake ciki yazo

Labarin halin da Bassey yake ciki dai ya zo ne bayan da wani mawaƙi Alexander Onyekachi mai amfani da @oc_cares1 a Instagram da wani maƙadi Bright Bassey mai amfani da @only1brytos a Instagram, suka ce sun dunga lura da ƙoƙarin da yake tun sanda ya koma unguwar a watan Disamban 2021.

Bright yace:

Mutane da dama sun riƙa ganin wannan mutumin na tsawon lokaci. A cikin watan Disamban da ya wuce muka koma Ajah (Legas). Tun daga wannan lokacin, ni da abokin aiki na mun riƙa ganin shi. Bamu taɓ sanin cewa babban ɗan wasa bane.

Mun yi zaton cewa ba kowa bane shi har sai da muka samu ƙarfin guiwar yin magana da shi. Mun ga wasu mutane a ciki sharhin da suka yi na cewa ba su yi tunanin zai iya yin magana da turanci ba.

Dan wasan kwallon kafa Ahmed Musa ya rabawa ‘yan kasuwa mutum 5,000 dubu ashirin-ashirin a garin Jos.

A wani labarin kuma Ahmed Musa ya gwangwaje ƴan kasuwa da dubu ashirin-ashirin a Jos.

Kaftin din Super Eagles, Ahmed Musa na ci gaba da tallafa wa al’ummar sa yayin da dan wasan ya bayar da gudummawar Naira 20,000 ga mutane kusan dubu biyar a garin Jos,domin habaka jarin kananun sana’o’in su.

Musa wanda ya shahara wajen taimaka wa gajiyayyu da marasa lafiya, inda ya mika kyautan naira 20,000 ga kowane mutum da kansa a garin Jos.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe