Tuni shirye-shirye su ka kankama dangane da auren dan Sanata Umar Kibiya, Amir Kibiya Usman da diyar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.
Kamar yadda shafin Fashion Series na Instagram ya bayyana, an ga cewa ranar 2 ga watan Satumba wato wata mai kamawa za a yi gagarumin shagalin.
Hotunan ankon bikin Rukayya sun bayyana wanda ake sa ran manyan mutane da ‘ya’yan hamshakan kasar nan za su halarta.
Za ayi daurin auren ne a fadar Sarkin da ke Kano kamar yadda aka gani a katin daurin auren.
Nan da nan mutane su ka bazama su na ta yi wa masoyan fatan alkhairi yayin da jama’a da dama su ke zaman jiran ganin hotunan auren.
Allah ya sanya alkhairi kuma ya nuna mana lokacin lafiya.
Ku ci gaba da bibiyarmu don LabarunHausa za ta tabbatar ta kawo muku hotunan shagulgulan auren kuma ta fede muku biri har wutsiyarsa.
Ga wallafar a kasa:
So makaho ne: Zukekiyar baturiya mai arziki ta zo har Najeriya inda ta yi wuff da gurgu
- Zukekiyar mata mai zama a Amurka mai suna Ranti Jacobs Agbaminoja da kuma Omotayo Agbaminoja sun nuna wa duniya cewa akwai soyayyar gaskiya har yanzu
- Ranti, wacce baturiya ce ta bayyana yadda ta fada tarkon soyayyar Omotayo wanda ya ke da matsalar kafa, hakan yasa ta zo Najeriya don aurensa
- Masoyan sun nunawa duniya cewa yadda ake kallo kamar kudi ne tushen soyayyarsu ba gaskiya bane don jajircewarsu ta wuce misali
Bayan sun yi auren kotu a 2015, wata baturiya mai suna Ranti Jacobs Agbaminoja ta zo har Najeriya don auren saurayinta, Omotayo Agbaminoja wanda gurgu ne inda aka yi shagalin a 2022, Legit.ng ta ruwaito.
Baturiyar wacce ke da tushen Yarabawan Najeriya ta sanar da BBC News Yoruba a tattaunawar da su ka yi da ita cewa sun hadu da Omotayo ne a wata coci da ke Maryland.
Daga fara abota da juna, sai su ka fara soyayya wacce duk da hakan bata taba tambayarsa yadda aka yi ya fara amfani da keken guragu ba.
Baturiyar wacce ‘yar jarida ce ta bayyana cewa dakansa Omotayo ya sanar mata yadda lokacin yana karami aka yi masa allurar foliyo wacce tayi sanadiyyar shanye masa kafafu.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com