Wata kyakkyawar mata ta rasa angonta bayan kwana goma sha biyu da aurensu da, Legit.ng ta ruwaito.
Duk da dai ba a samu cikakken bayani dangane da silar mutuwarsa ba amma an ga yadda bidiyon bikinsu ya dinga yawo a TikTok bayan @glorcycutex3 ta wallafa.
An samu bayanai akan yadda aka gudanar da auren ranar 26 ga watan Mayu sannan bayan kwana biyu da daurin auren aka ci gaba da shagulgula irin na al’ada.
A cikin bidiyon an ga masoyan sanye da fararen kaya yayin da su ke cikin mota daga bisani kuma an hasko sauran wurare har da inda aka mikawa amaryar abin magana.
Sai dai ranar 9 ga watan Yuni, kwana 12 kenan da daurin auren, angon ya kwanta dama.
Tuni mutane su ka dinga bude bidiyon wanda yanzu haka fiye da mutane miliyan 7.2 sun bude shi su na ta masa addu’o’i da fatan samun rahamar Ubangiji.
Bidiyon wata Amarya tana kwasar rawa a liyafar aurensu yayin da ango ya zauna takaici ya ishe shi
A wani guntun bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani an ga inda amarya ta zage a liyafar aurenta tare da kawayenta tana kwasar rawa yayin da angonta ya shiga damuwa, Shafin Arewa Fashion Style ne ya ruwaito.
Tun a bidiyon idan mutum ya kula zai ga yadda angon ya koma kan kujera ya zauna yayi tagumi da alamu duk abin duniya ne ya ishe shi.
Ita kuma amaryar ta ci gaba da rawarta inda ta nuna halin ko in kula tare da kwayenta.
Mutane da dama sun yi tsokaci yayin da suke cewa ta yiwu angon yana jin haushin rawar tata ne ko kuma dai bai san zata iya wannan rawar haka ba.
Ga bidiyon a kasa:
Tsokacin jama’a
Labarun Hausa ta samu nasarar tattaro wasu daga cikin tsokacin mutane karkashin bidiyon:
Farfesa Bello Wakili Galadanci ya ce:
“Ango Bai so wannan show din ba zako tayi bayani da manyan baki.”
Abu Dhalib Bin Mustapha yace:
“Kunga illar Auren yar TikTok koh.”
Hizbullahi Murtala yace:
“Angon yana ta sauya tunani. Allah ya kyauta.”
Mariam Gimbiyo Oloyede tace:
“Angon yana cewa a ransa: Shin a wacce cakwakiya nasa kaina.”
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com