Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya naɗa kakakin yaƙin neman zaɓen sa na neman takarar shugabancin ƙasar nan.
An bayyana sunayen mutanen da ya naɗa
Atiku Abubakar ya naɗa Dino Melaye da Daniel Bwala a matsayin kakakin yaƙin neman zaɓen sa. Jaridar The Punch ta rahoto.
Mai taimaka wa Atiku kan harkokin sadarwa, Paul Ibe, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Alhamis.
Ibe yace nan take naɗin ya fara aiki.
Asalin mutanen da ya naɗa kakakin yaƙin neman zaɓen sa
Dino Malaye, tsohon sanata a majalisar dattawa ta 8, haifaffen jihar Kogi ne. Ya wakilci Kogi ta Yamma a majalisar dattawa.
Daniel Bwala, wanda kafin zuwa yanzu, babban ƙusa ne a jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC), lauya ne kuma haifaffen jihar Adamawa.
Atiku na ƙara wa tawagar yaƙin neman zaɓen sa ƙarin mutane
Atiku Abubakar ba a jima ba ya naɗa Lynne Bassey a matsayin mai taimaka masa na musamman kan batun jinsi da cigaban mata.
A ranar 5 ga watan Yuli, 2022, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara mutum uku masu taimakawa kan harkokin sadarwa a tawagar yaƙin neman zaɓen sa.
Mutum ukun da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara sun haɗa da: Eta Uso, Abdulrasheed Shehu da Demola Olanrewaju.
2023: Kungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna kasashen waje ta lashi takobin tara kudade don tallafawa Atiku a zabe mai gabatowa
A wani labarin kuma, wata ƙungiyar ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta sha alwashin tara kuɗaɗe domin tallafawa Atiku Abubakar a zaɓe mai zuwa. Atiku na neman ɗarewa kujerar shugabancin ƙasar nan a babban zaɓen dake tafe na shekarar 2023.
Wata kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, ga me da harkar siyasa mazauna kasar waje (DVND) ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, bayan ta sha alwashin tara kudade domin tallafawa.
Ƴan Najeriya mazauna kasashen waje sun kuma ce takarar Atiku ya kara musu kaimin son kada kuri’a a zabe mai zuwa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com