Hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a Jihar Kano, KAROTA ta yi ram da wani matashi wanda ya ke anfani da sunanta wurin yin yadda yaso, DalaFM ta ruwaito.
Yana tsaka da tare motoci a kan titi da misalin karfe sha biyu na daren Litinin akan yi ram da shi don yayi karin bayani.
Kakakin hukumar, Nabulisi Abubakar kofar Na’isa ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.
Ya bayyana cewa da zarar sun kammala duk wasu bincike akansa za su mika shi ga ‘yan sanda don gurfanar da shi gaban kotu da kuma fadada bincike.
Ya kara da cewa hukumar ta dade da samun labari akan yadda matashin yake amfani da sunanta wurin takurawa da cutar da jamai’a, sai yanzu ne dubunsa ta cika.
Kamar yadda bayanai su ka nuna, sunan matashin Lukman Abdullahi, shekarunsa 27 kuma yana zama a Unguwar Sabon Gari ne.
Ya tabbatar da cewa shi din asalin dan Maiduguri ne sannan yana amfani da kayan jami’an Karota ne don yayi yadda yaso a matsayin ma’aikacin hukumar.
Yadda matashi ya halaka mahaifinsa kan rikicin gona a Nasarawa
Mutanen garin Masaka a cikin ƙaramar hukumar Karu ta jihar Nasarawa a ranar Litinin, sun shiga cikin ruɗani da tashin hankali bayan wani matashi ɗan fari Tunde Badejo ya halaka mahaifinsa Badejo Idowu saboda taƙaddama akan gona wacce mallakar iyalan gidan ce.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Tunde ya addabi mahaifin na sa kan ya mallaka mishi wani yankin ƙasar gonan tun sama da shekara ɗaya nan baya.
An bayyana yadda matashin ya aikata wannan ɗanyen aikin
Matar mamacin, Madam Tolani Badejo, ta shaida wa wakilin jaridar yayin da ya ziyarci wurin da abun ya faru cewa mijinta ya roƙi Tunde ya ba shi lokaci domin raba gonar cikin adalci ga dukkan iyalan gidan.
Madam Tolani ta ce:
Tun shekarar da ta gabata yake damun mijina kan maganar gonar, to a ranar Litinin lokacin da suka samu saɓani na ƙarshe, sai ya zaro wuƙa ya daɓa wa mahaifinsa a wurare daban-daban.
Ya daɓa masa wuƙa a kai, wuya, ƙirji, hannuwa da ƙafafu har sai da ya halaka shi. Na nemi ɗauki amma tuni ya tsere.
An miƙa lamarin zuwa ga hukumar ƴan sanda
Ayomide Badejo, ɗa na biyu ga mamacin, ya bayyana cewa tuni suka miƙa rahoton lamarin da ya auku ga hukumar ƴan sanda yayin da aka kai gawar mahaifin su ɗakin ajiyar gawarwaki.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com