34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Matar aure ta ɗauko hayar sa-ɗaka da zata riƙa gamsar da mijinta, ta sanya mata albashi mai tsoka

LabaraiMatar aure ta ɗauko hayar sa-ɗaka da zata riƙa gamsar da mijinta, ta sanya mata albashi mai tsoka

Wata matar aure mai shekaru 44 mai suna Pattheema, ta ɗauki hayar sa-ɗaka domin taimaka mata wurin gamsar da mijinta saboda ita ta kasa gamsar da shi.

Bidiyon ta na neman sa-ɗakar ya tada ƙura

Shafin Yabaleftonline ya tattaro cewa Patteema ta jawo cece-kuce a yanar gizo bayan taje TikTok inda ta tallata wannan baƙon aikin na neman sa-ɗaka guda uku domin gamsar da mijinta.

Matar auren ta bayyana sharuɗɗan aikin

A cikin bidiyon da ta fitar, tace duk masu sha’awar aikin dole ne su kasance masu shekaru 30 zuwa 35, sannan sun kammala karatun kwaleji ko digiri.

Dole ne kuma an gwada matan domin duba lafiyar su ta yadda ba su ɗauke da cutar ƙanjamau ko wasu cututtukan.

Ta ƙara da cewa:

Za a biyaki aƙalla £340 (kimanin N145k) a wata, zaki samu wurin kwana da abinci kyauta. Amma zaki taimaka min. Biyu daga ciki zasu taimaka min da aiki kan takardu a ofishina. sannan ɗayar kuma zata kula dani, mijina da yarana.

Ba za tayi kishi da sa-ɗakar ba

Patheema tace ba wani kishi tsakanin ta da matan, sannan mijinta na da ƴancin zaɓar wacce yake son kwanciya da ita a koda yaushe.

Ina mai bada tabbacin cewa faɗa ba zai shiga tsakani na da ke ba. Zan bar mijina ya zaɓi wacce yake son kwanciya da ita ko ya zauna da ita. Ba raba lokaci, zai zaɓa da kansa.

An tattaro cewa yanzu haka ta ɗauko hayar wata budurwa mai shekaru 33 domin shigowa cikin gidan a matsayin sa-ɗakar mijinta.

Pattheema tace duk da cewa budurwar ba wacce mijinta yayi tsammanin samu bace, ya amince ta zama ‘ƙaramar matar sa’. Ta kuma rufe ɗaukar aikin.

Yadda na dawo da budurwar mijina gidana don mu ci gaba da faranta masa rai tare, Matar aure

A wani labarin kuma wata matar aure ta bayyana yadda ta dawo da budurwar mijinta gidanta domin su cigaba da farantawa mijinta rai.

Wasu mata biyu a kasar Kenya sun bayyana yadda yanzu haka suke zama a gida daya tare da mijinsu, Abraham, Legit.ng ta ruwaito.

Sarah da Maureen suna zama ne a matsayin kishiyoyi bayan Abraham ya auresu gaba daya, kuma suna nuna wa juna so da kauna tamkar ‘yan uwa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe