31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Akwai masu bin baki: Bidiyon karamar yarinya a Dubai tana yi wa su Maryam Yahaya turanci

LabaraiKannywoodAkwai masu bin baki: Bidiyon karamar yarinya a Dubai tana yi wa su Maryam Yahaya turanci

Wani bidiyo ya yi matukar daukar hankula wanda aka ga jarumar Kannywood, Maryam Yahaya, Minal Ahmed, Momi Gombe da wata kawarsu mai suna Maryam su na ta turanci tare da wata karamar yarinya, shafin Real Ado Gwanja na Facebook ne ya ruwaito.

Da alamu sun dauki hankalin yarinyar ne wanda hakan yasa ta kasa hakuri har sai da tayi musu magana.

Kamar yadda yarinyar tace, sunanta Rumaisa inda ta bukaci su gabatar mata da kawunansu daya bayan daya.

Ta ce sun burgeta, kuma zata so sanin daga inda suke. Anan ne su ka sanar da ita cewa daga Najeriya su ke, ita kuma ta fada musu daga Pakistan take.

Ta ci gaba da jan zancen da tsawo har take cewa Najeriya a Nahiyar Afirka take koh?

Bidiyon ya yi matukar daukar hankalin mutane. Amma dai wasu suna ganin bin baki jaruman suke yi don da alamu Minal ce kadai ta iya tabuka turancin dakyau.

Ga bidiyon a kasa:

https://fb.watch/eGs5HpLIOn/

Tsokacin jama’a karkashin bidiyon

Ga tsokacin mutane karkashin bidiyon:

Fadila H Aliyu tace:

“Sai wow wow su ke yi.”

Saman Na Ta’ala yace:

“Mafi yawan masu kwament anan din ma ba turancin suke ji ba duk yan kano ne.”

Yahuza A Hassan yace:

“Zanso ace Musa mai sana’a na nan.”

Umar Attahir yace:

“Wasu na cin baki.”

Bin Isma yace:

“What is your name kawai Maryam yahaya ta sani! Anata zubo turanci sunyi shiru sai yake suke, Minal ce me kokarin amsawa. Su momi sai washe baki ake kamar ana shooting.”

Aliyu Muhammad Bashir yace:

“Alamu sun Nuna Maryam Yahaya da momy befi sau uku-uku su ka je primary school ba.”

Abubakar Muhd Olan yace:

“Minal ce kadai ta iya yaren dakyau, sauran duk bin baki su ke yi. Lamarin ya bani dariya.”

Sabbin hotunan Maryam Yahaya a Dubai babu rigar mama sun janyo mata zagi

A ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairun 2022 jarumar Kannywood, Maryam Yahaya ta saki sabbin hotunan ta a shafin ta na Instagram ba tare da ta sanya rigar mama ba.

Hotunan sun janyo mata suka da caccaka ko ta ina kafar inda wasu suka dinga zagin ta akan yadda bata dade da murmurewa daga ciwo ba ta fara shigar banza.

Wasu sun dinga yi mata wa’azi suna cewa ya kamata ta yi wa kanta fada ta daina duk wasu ayyuka marasa kyau musamman ganin ko jikin ta bata gama mayarwa ba.

A kwanakin baya jarumar ta yi ciwo wanda mutane da dama suka zaci mutuwa zata yi don duk ta rame ta fita hayyacin.

A lokacin, masoyanta sun dinga yi mata fatan alkhairi da kuma fatan zata natsu, ciwon ya zama izina a gare ta ta gyara rayuwar ta.

Ba wannan bane karon farko da jarumar ta saba yin hotuna ba tare da ta sanya rigar mama ba. Ga masu bibiyarta a Instagram, ta kan saki bidiyoyi ko kotuna sanye da riguna da suke tabbatar da hakan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe