Jagoran tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya nemi da ya tallafawa wani tsohon ɗan wasan Najeriya, Bassey Etim, wanda aka gani a yankin Ajah a jihar Legas yana cike ramuka a titi.
Wanda ake ma laƙaɓi da ‘Iron bar’ tsohon mai daga ƙarfen, an dai ganshi ne a wani wuri inda hanyar Ado/Badore ta lalace a cikin Legas.
An ci karo da shi yana gyaran ramuka a titi
Jaridar Sportsbrief ta tattaro cewa wani mawaƙi ɗan Najeriya mai suna Oc Cares ya bayyana yadda ya ci karo da tsohon ɗan wasan akan titi na tsawon lokaci, wanda hakan ya sanya ya tuntuɓe shi.
Bassey Etim, wanda ya lashe zinare a wasannin Commonwealth na shekarar 1983 a Malta, ya bayyana cewa ya samu rauni ne yayin da yake wakiltar Najeriya a gasar Olympics na 1984.
Ya koka kan yadda Najeriya tayi watsi da shi
Etim mai shekaru 56, yace sai da ya ƙarar da dukkanin ƴan kudaden sa wurin neman magani, inda yace Najeriya tayi watsi da aji.
Na samu rauni, sannan bayan na dawo, Najeriya taƙi kula da rauni na, hakan yasa na kwashe abinda na tara na koma Amurka a Satumban 1985 domin kula da rauni na.
Amma duk da haka na sake miƙa kaina domin taimakawa ƙasa ta.
Mutane na cewa meyasa za kayi hakan? Bayan sun ƙi kula da kai?
Ahmed Musa ne neman shi domin taimakon sa
Bidiyon wanda tuni ya ƙarade yanar gizo, ya ɗauki hankalin Ahmed Musa, wanda ya nemi samun yadda za su haɗu.
Ɗan wasan gaban na kulob ɗin Fatih Karagumruk ya rubuta:
Dan Allah ta ya zan iya haɗuwa da shi
Ahmed Musa ya gwangwaje tsohon ɗan wasan Super Eagles da naira miliyan 2
A wani labarin kuma Ahmed Musa ya gwangwaje tsohon ɗan wasan Super Eagles da maƙudan kuɗi.
Tsohon ɗan wasan Najeriya, Kingsley Obiekwu, ya miƙa saƙon godiyar sa ga kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, da ɗaukacin ‘yan Najeriya bisa kulawar da su ka nuna masa bayan rahotannin cewa yana cikin halin matsin rayuwa.
Obiekwu ya bayyana cewa ya shiga sana’ar tuƙin motar haya ne domin ya ƙara kan kuɗaɗen da ya ke samu a harkar kocin ‘yan wasa. Jaridar Punch ta ruwaito
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com