29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Sarkin Shaidanu: Mutumin da ya auri mata 57 a Enugu

LabaraiSarkin Shaidanu: Mutumin da ya auri mata 57 a Enugu

Ana kiransa da mutum mai hatsari, ko Solomon din zamaninmu; kuma hakan ba kuskure bane. Da kanshi yake kiran kanshi da ‘Sarkin shaidanun duniya’.

Dangane da Dr Simon Odo alias Onuwa, sarkin shaidanun duniya, na garin Aji, cikin karamar hukumar Igbo-Eze ta kudu dake jihar Enugu, duniya a tafin hannunsa take.

Shu’umancinsa na bawa mutane mamaki

Jama’ar garinsu da na makwabta suna mamakin irin shu’umancinsa, wanda yanzu haka ya auri fiye da mata 50. Duk da shekarun Onuwa 72, amma har yanzu bai gama auren mata da haihuwar yara ba don ya auri mata ta 58. Kuma babu wata matar da yake yi wa asiri don ya aureta.

Sarkin Shaidanu | Photo credit: Vanguard
Sarkin Shaidanu | Photo credit: Vanguard

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta sake kara farashin wutar lantarki

Yawan iyalina yasa za mu iya kada dan takara ko mu saka ya ci zabe

Yayin da wakilin Sun news online ya kai wa kasurgumin bokan ziyara a kauyensa, Aji, ya yi masa alfaharin cewa shi da yaransa za su iya zaben duk wani dan siyasa da ya tsaya takara kuma ya samu nasara saboda yawansu. Kuma za su iya kayar da duk wani dan takara idan suka bukaci yin hakan.

A cewarsa, yana da jikoki fiye da 200, yaransa sun fi 300, sannan matansa 57. Hakan zai ba shi damar kayar da dan takara ko kuma zabensa.

Ya ce shi cikakken mabiyin addinin Kirista ne a baya, amma ya koyi harkar maganin gargajiya ne tun bayan yayi wasu ciwuka masu firgitarwa na tsawon shekaru, kuma ya samu waraka a Ijebu-Ode.

Daga nan ne ya koyi bayar da magunguna daga wata tsohuwa a 1962. Hakanan ya koya duk da iyayensa basu so ba, amma tsoro ya hanasu hanashi koyo.

Ya kuma bayyana yadda ba zai taba barin yaransa maza su yi aure-aure ba. Saboda babu wanda zai iya dagewa da jajircewa cikinsu kamar shi. Ya ce a duk matansa 57, 2 ne kawai basu haihu ba.

KU KARANTA: Atiku ya siyar hannun jarinsa na Intel, ya dora laifi a kan gwamnatin Buhari

Tsabar shu’umanci na da bin hanyar shaidan ce ta sanya ake mini lakabi da sarkin shaidanu

Da aka tambaye shi dalilin da yasa ake kiranshi sarkin shaidanu, ya ce saboda tsabar shu’umancinsa da bin turbar shaidan ne, ta hanyar aure-aure, duk da baya zina.

Amma yana farin cikin yadda ba ya bayar da magungunan kashe wani ko cutar da wani.

Ya kuma bayar da labarin yadda yake yanka wa iyalinsa shanu ko wanne wata don su ci kuma su more, sannan duk matansa masu ilimi ne, da yawansu suna koyarwa a makarantun da ya gina a anguwarsu.

A wani labari na daban, Sanata mai wakiltar Borno ta kudu kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan harkar sojoji, Mohammed Ndume yace shugaba Muhammadu Buhari ya sauya dukkan ministocinsa da sauran jiga-jigai da ya nada, matsawar yana yi wa ‘yan Najeriya fatan alheri a 2021.

Duk da Ndume ya ce Buhari mutumin kirki ne, amma yana zagaye ne da wadanda basa fatan ganin cigaban Najeriya, Vanguard ta wallafa.

Sanata Ndume ya fadi hakan ne jiya, yayin tattaunawa da manema labarai a gidansa dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe