
Wani dan Najeriya mai suna Lawson ya yi nasarar samun gurbin karatu a kasar waje inda ya nuna farin cikin sa a shafin sa na Twitter musamman. Bikin nasarar sa ya bazu sako da lungu,a shafin Twitter.
Sai anjima ASUU sai anjima Najeriya
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, saurayin da ya samu nasarar karatu a Turai ya yi bankwana da ASUU da kuma Najeriya.
A cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Twitter,an gan shi ya durkusa ya na nuna godiyan sa ga Allah da ya yi nasarar samun karatu a kasar waje.
Lawson yayi godiya sosai
Idan aka duba tweet dinsa zai bayyana dalilin da ya sa yake godiya da cewa ya tsere ASUU. In ba a manta cewa ba Ma’aikatan Jami’o’i sun kwashe sama da watanni 5 suna yajin aiki. Daliban Najeriya da dama na gida cikin takaici, don haka samun karatun Lawson a kasar waje, mutane za su fahimci irin farin cikinsa da yake ciki.
Martanin masu amfani da shafukan sada zumunta
@Princes62118111 sun ce: “Bye bro… incase idan za ka dawo Najeriya, pls ka siyo min biredi.”
@hayordaniel yayi sharhi: “Wannan abu yazo ya zama kamar nasara amma ba nasara ba. Amma dai nasarar ce. “
@BiggerKiing ya ce: “Ikon Allah ji yadda mutane ke tayasa murna dan ya bar kasar sa, don Allah a tuna da Najeriya Allah yasa ta zama babban wuri.“
Dan tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido ya fita da ajin farko (First Class ) a jami’ar Portsmouth dake birnin Landan
Mai martaba tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido, tare da mai martaba sarkin Zazzau ambasada Nuhu Bamalli, sun halarci bikin kammala karatun dan tsohon sarki Sunusin, mai suna Mustapha Lamido Sanusi.
Sakamakon da dan sarki Sunusi Lamidon ya samu
An tattara rahoton cewa, Mustapha din ya fita da sakamako ajin farko, wato (first class ) a fannin ilimin tattalin arziki, a wata jami’a Portsmouth dake birnin Landan.
A lokacin bikin, sarkin yayi kira ga yaron da ya kammala digirin, da yayi amfani da ilimin nasa wajen samar da cigaba da tallafawa marasa karfi.
Dalilin neman ilimi , inji sarki Sunusi
A fadar sa, yace babban dalilin da yasa ake yin ilimi shine domin a kyautata gobe, da kuma yin hidima ga al’umma.
Da take nagana a yau, sarkin ya ce, Mustapha din ya yi nuna hazaka da ta daga darajar Najeriya, inda ya kara da cewa, dukkanin dalibai da suke karatu a kasashen waje, suyi Koyi da shi domin su fita da kyakkyawan sakamako.