Gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta kare matakin ta na fitar da N1.15bn domin siyan motoci ƙirar SUV guda 10 ga jamhuriyar Nijar, inda take cewa tayi hakan ne domin taimakawa ƙasar tsare iyakokinta domin ingantuwar tsaron Najeriya.
Da take amsa tambayoyi a faɗar shugaban ƙasa bayan, ministan kuɗi, Zainab Ahmed, tace ba wannan bane karon farko da Najeriya ke taimakon makwabtan ta ba. Jaridar The Punch ta rahoto.
Ta haƙiƙance cewa shugaban ƙasa yana da damar ɗaukar waɗannan matakan domin amfanuwar ƙasar.
Shugaba Buhari ya amince da siyo motocin
Wani rahoto da aka fitar ranar Laraba a jaridar Sahara Reporters a watan Yuni, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da N1.15bn domin siyan motoci guda 10 ƙirar Toyota Land Cruiser V8 ga gwamnatin Nijar.
Wasu bayanai da aka samo daga shafin yanar gizon ministirin kuɗi sun nuna cewa a watan Yulin 2022, an amince da fitar N1,145,000,000 domin biyan kamfanin Kaura Motors Nigeria Limited domin samar da motocin ƙirar SUV.
Bayanan sun kuma nuna shugaba Buhari ya amince da fitar da kuɗin tun watan Fabrairun 2022.
Labarin dai ya fusata dubbunan ƴan Najeriya waɗanda ke ganin cewa fitar da kuɗi domin wata baran ƙasa ba abinda yakamata ace gwamnati ta mayar da hankali akai bane duba da halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki.
Ta kare gwamnatin tarayya kan matakin da ta ɗauka na siyo motocin
Da take kare matakin na gwamnatin tarayya, ministan kuɗi tace:
Bari na ce kawai, a lokuta daban-daban Najeriya na buƙatar taimakon maƙwabtan ta musamman na kusa-kusa, domin taimaka musu wurin kare ƙasashen su saboda yana da alaƙa da mu.
Wannan ba shine karon farko ba da Najeriya ta taimaki ƙasashen Nijar, Kamaru ko Chadi ba, sannan shugaban ƙasa ya duba yaga abinda ake buƙata, bisa roƙon da shugaban ƙasan su yayi, sannan irin wannan roƙon ana amincewa da shi, sannan taimakon da aka bayar an bada ne domin bunƙasa ikon su na kare ƙasar su domin hakan na da alaƙa da tsaro da kuma Najeriya.
Ƴan Najeriya na da damar yin tambayoyi, amma shugaban ƙasa yana da alhakin yin duba kan abinda zai zama mafi kyau ga ƙasar nan. Ba zan iya ja da wannan matakin na sa ba.
Gwamnatin tarayya zata kara kashi 5% na haraji kan kiran wayan salula
Nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara biyan harajin kashi 12.5 na ayyukan sadarwa a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke shirin kara harajin kaso biyar wanda ya hada da ayyukan sadarwa a Najeriya.
Ministar kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da haraji kan ayyukan sadarwa a Najeriya ranar Alhamis a Abuja.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com