27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Ban taɓa ganin lusarin shugaban ƙasa irin Buhari ba -Salihu Tanko Yakasai

LabaraiBan taɓa ganin lusarin shugaban ƙasa irin Buhari ba -Salihu Tanko Yakasai

Ɗan takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Salihu Tanko Yakasai, ya yiwa shugaba Buhari wankin babban bargo kan yadda ya ƙyale mutanen da ya naɗa muƙamai ke ƙin bin umurnin sa ba tare da ya hukunta su ba.

Ya caccaki Buhari kan ƙin yin komai bayan ƙarewar wa’adin kawo ƙarshen yajin aikin ASUU da ya bada

Salihu Yakasai ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter bayan ƙarewar wa’adin sati biyu da shugaba Buhari yaba ministan ilmi, Adamu Adamu na tabbatar da cewa an kawo ƙarshen yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’a (ASUU) ke yi.

Malaman jami’o’i na cigaba da yaji aiki. A ranar Litinin 1 ga watan Agusta, suka ƙara wa’adin sati huɗu domin cigaba da yajin aikin.

Da yake mayar da martani kan ƙara wa’adin yajin aiki, ya rubuta cewa:

Ban taɓa ganin lusarin shugaban ƙasa irin shugaba Buhari ba. Zai bayar da umurni ga mutanen da ya naɗa sannan suyi watsi da shi ba tare da ya hukuntansu ba. Ya bayar da wa’adin sati biyu a kawo ƙarshen yajin aikin ASUU, ba wanda ya ɗauke shi da muhimmanci sannan lokacin har ya wuce. A taƙaice a iya cewa wannan babban abin kunya ne.

Buhari bai san da barazanar ƴan ta’adda na sace shi ba har sai da na gaya masa -El-Rufai

A wani labarin kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa shugaba Buhari bai san da barazanar ƴan ta’adda ta sace ba har sai da ya gaya masa.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya bayyana cewa shine wanda ya sanar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari batun barazanar ƴan ta’adda ta sace shi.

A wani bidiyo da aka saki a ƙarshen mako, ƴan ta’addan waɗanda suka sace fasinjojin jirgin ƙasa a watan Maris, sun yi barazanar sace shugaba Buhari da El-Rufai.

Da yake magana a wani shiri a gidan rediyo wanda wakilin jaridar ya bibiya a daren ranar Laraba, gwamnan yace shi kan shi an gargaɗe shi kan tsoma iyalan gidan sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe